Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata sauya sunan hanyar Murtala Mohammed dake Abuja

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Gwamnatin Tarayya ta musanta jita-jitar cewa ta canja sunan hanyar Murtala Mohammed dake Abuja zuwa Wole Soyinka.

Wata sanarwa da mai taimaka wa ministan harkokin yaɗa labarai da haɗin kan ‘yan ƙasa, Rabi’u Ibrahim ya fitar ranar Litinin, ta ce gwamnatin Shugaba Tinubu bata taɓa yunƙurin sauya sunan hanyar ba.

A ƴan kwanakin nan ne aka samu jita-jitar sakamakon buɗe wata sabuwar hanya da gwamnatin tayi wacce ke daga Katampe zuwa Jahi inda ministan Abuja, Barista Nyesom Wike ya shawarci shugaba Tinubu da a sa sunan Wole Soyinka wa hanyar, kuma ya amince da hakan.

Sanarwar ta kuma yi kira ga al’umma da su ƙaryata tare da kore duk wani batu dake cewa an sauya sunan hanyar, sannan kuma ta ƙara da cewa wannan aikin wasu ƴan adawa ne ga Gwamnatin Shugaba Tinubu.