Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Litinin, 31 ga Maris, da Talata, 1 ga Afrilu, 2025, a matsayin ranakun hutu domin bikin ƙaramar Sallah.
Ministan harkokin cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hakan a madadin gwamnati, inda ya taya al’ummar musulmi murnar kammala azumin Ramadan.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a Abuja, ministan ya buƙaci musulmi da su rungumi halaye na haƙuri, tausayi, karimci da zaman lafiya. Ya jaddada muhimmancin soyayya, yafiya da haɗin kai domin gina al’umma mai ɗorewa.
Har ila yau, ya buƙaci ‘yan Najeriya da su yi amfani da wannan lokaci domin yin addu’a na zaman lafiya, kwanciyar hankali da cigaban ƙasa.
Tunji-Ojo ya yi fatan cewa bikin Eid-el-Fitr zai ƙara danƙon zumunci da haɗin kai tsakanin mutane, ba tare da la’akari da bambance-bambancen addini da kabila ba.
A ƙarshe, ministan ya bukaci jama’a da su gudanar da bukukuwan sallah cikin lumana da kiyaye dokoki, tare da tuna da mabuƙata ta hanyar kyauta da taimako, domin raya ainihin manufar Ramadan da bikin Sallah.