Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da shafin rejista ga matasa masu noma don bada tallafi na musamman a wani shiri na yaƙi da matsalar rashin aikin yi da ƙarancin abinci a faɗin ƙasar nan.
Ministan cigaban matasa, Kwamared Ayodele Olawande ne ya sanar da ƙaddamar da shirin yayin wani biki a Abuja. Shirin, wanda aka ƙirƙira tare da haɗin gwiwar shirin bunƙasa tattalin arzikin matasa na Najeriya (NIYEEDEP), zai samar da damammaki na bunƙasar tattalin arziki ga matasa da kuma ƙarfafa ɓangaren noma a faɗin ƙasar.
Shirin zai samar da ayyukan yi har miliyan 6 ga matasa a shekarar 2025 a ɓangaren noma, samar da abinci, abubuwan sha, da kuma sarrafa taki domin magance matsalar rashin aikin yi ga matasa, rage talauci, kawo ƙarshen yunwa da wadata ƙasar da abinci, waɗanda a yau suke barazana ga tsaron ƙasarmu.
Shirin zai shafi matasa daga shekaru 18 zuwa 35 inda zasu samu lamuni da kuma abubuwan da suke buƙata dan inganta noma da samar da abinci. Hakazalika akwai horo na musamman akan noman zamani da kuma tallafi don inganta noman.
“Wannan shiri ba wai don ƙara samar da abinci ba ne kawai, a’a an samar da shi ne domin ƙarfafawa matasa ‘yan Najeriya da ba su ƙwarin guiwa, da kuma samar da ayyukan yi a karkara da birane, tare da tabbatar da walwala da tsaron ‘yan ƙasar,” in ji Kwamared Olawande.
Ya kuma yi kira ga matasa a faɗin ƙasar nan da su yi amfani da wannan damar wajen cicciɓo da makomar noma tare da bayar da tasu gudunmawar ga ci gaban kasar ta shafin yanar gizo dake ƙasa: www.niyeedep.org.