Gwamnatin Tarayya ta karɓe asibiti a Gombe da mayar da shi Cibiyar Lafiya ta Tarayya

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnatin Tarayya ta sauya Asibitin Janar dake garin Kumo a Jihar Gombe zuwa Cibiyar Lafiya ta Tarayya (FMC).

Kakakin Shugaban Bola Tinubu, Bayo Onanuga ya faɗi hakan a wata sanarwa, ranar Lahadi, inda ya ce FMC Kumo shi ne asibitin tarayya na biyu bayan Asibitin Koyarwa dake Birnin Gombe a jihar.

Ya ce, sauyin zai sanya asibitin ya zama babbar cibiyar kula da lafiya a jihar ta yadda za a samar da yanayi na bada horo ga jami’an lafiya da kuma bunƙasa harkar kula da lafiya a jihar da ma Arewa ta Gabas baki ɗaya.

Rahotonni sun bayyana cewa, Gwamna Inuwa Yahaya na jihar ne ya nemi Gwamnatin Tarayya da ta karɓe iko da asibitin, inda Shugaba Tinubu ya amince da hakan la’akari da gazawa da ɓangare kula da jarirai ke fama da shi wanda ke sabbaba yawan mutuwar su a shiyyar.

Haka kuma, Gwamnatin Tarayya ta yi la’akari da ƙoƙarin Gwamnatin Jihar wajen inganta harkokin kiwon lafiya, wanda ya dace da Ajendar Sabonta ƙasa na gyare-gyare a fannin lafiya.