Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Bankin Keystone ya tabbatar da cewa a halin yanzu ya zama mallakin Gwamnatin Tarayyar Nijeriya, inda ya bayyana cewa karɓe shi zai ƙara inganta harkokinsa da kuma sauƙaƙa hanyoyin dawo da jarin waje.
Bankin ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Instagram a yammacin ranar Talata, biyo bayan hukuncin da babbar kotun jihar Legas, Ikeja ta yanke.
Kotun ta bayar da umarnin a kwace hannun jarin da tsoffin masu hannun jarin bankin ke da su a baya, tare da miƙa hannun jari ga gwamnatin tarayya yadda ya kamata.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “Bankin Keystone Bank yana so ya fayyace rahoton kafafen yaɗa labarai kan hukuncin da kotun hukunta manyan laifuka ta jihar Legas, da ke zaune a Ikeja, Legas, a ranar Talata, 11 ga Fabrairu, 2025, game da matsayin tsoffin masu hannun jarin bankin: Sigma Golf Nigeria Limited da Alhaji Umaru H. Modibbo,” inji sanarwar.
“A zaman kotun a ranar 11 ga watan Fabrairu, 2025, kotun ta bayar da umarnin a kwace hannun jarin bankin da waɗannan masu hannun jarin suka mallaka a baya domin samun goyon bayan gwamnatin tarayyar Nijeriya,” inji ta.
Bankin ya bayyana ci gaban a matsayin wani muhimmin ci gaba, wanda ke ƙarfafa harkokinsa da kuma sanya shi don ci gaba na dogon lokaci.