Gwamnatin Tarayya ta kashe biliyan N8.8 wajen gyaran wutar lantarkin da aka riƙa lalatawa a 2024 – TCN

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sule Abdulaziz, Manajan Darakta na Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Nijeriya (TCN), ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta kashe kimanin Naira biliyan 8.8 wajen gyaran turakun wutar lantarki da aka lalata a sassa daban-daban na ƙasar.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin Mr. Abdulaziz, wanda aka wakilta ta hannun Mr. Olugbenga Ajiboye, Daraktan Gudanarwa na Mai Samar da Ayyukan Rarraba Wutar Lantarki (TSO), a yayin taron kwata-kwata na Rukunin Aikin ɓangaren Wutar Lantarki da aka gudanar ranar Talata a birnin Abuja.

Ya bayyana cewa an lalata jimillar turaku 128 daga watan Janairu 13, 2024, zuwa yanzu, ta hannun masu lalata kayayyakin gwamnati da ‘yan bindiga. 

Ya koka kan yadda ake ci gaba da lalata muhimman kayayyakin more rayuwa da kuma rashin tasirin matakan shari’a kan masu aikata laifin da aka kama.

Abdulaziz ya kuma bayyana ƙalubalen da TCN ke fuskanta wajen dawo da muhimman layukan wutar lantarki, kamar layukan Shiroro-Mando-Kaduna. 

Ya ƙara da cewa kamfanin ya tilasta ɗaukar sojoji don rakiyar kwangiloli saboda matsalolin tsaro.