Gwamnatin Tarayya ta raba tallafin kayayyaki ga waɗanda ambaliya ta shafa a Keffi

Gwamnatin Tarayya ta raba tallafin kayayyakin abinci ga ahali 450 waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Ƙaramar Hukumar Keffi, Jihar Nasarawa.

Gwamnati ta yi rabon kayan ne ta hannun Ma’aikatar Jinƙai, Agaji da Bunƙasa Zamantakewa ƙarƙashin jagorancin Minista Sadiya Umar Farouq wadda kuma Kwamishinar Tarayya, Imam Sulaiman Ibrahim ta wakilta.

Yayin rabon tallafin

Kayan tallafin da aka raba wa waɗanda lamarin ya shafa a ranar Lahadi, sun haɗa da buhuhunan shinkafa, katan-katan na tumatiri, man girki haɗa da tufafi da sauransu.

Waɗanda aka gani a wajen rabon tallafin wanda ya gudana a yankin GRA, har da nakasassu da marasa galihu.

Sa’ilin da take jawabi a wajen taron, muƙaddashin Minista Sadiya, Iman Sulaiman Ibrahim, ta isar da saƙon fatan alheri na Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da Minista Sadiya ga waɗanda ambaliyar ta shafa.

Yayin rabon tallafin

A hannu guda, a lokacin da suke karɓar kayayyakin a madadin waɗanda suka ci gajiyar tallafin, ɗan majalisar dokokin jihar mai wakiltar Keffi ta Gabas, Honarabul Abdulazeez SK Danladi, da takwaransa mai wakiltar Keffi ta Yamma, Honarabul Baba Ali Nana, sun yaba wa Shugaba Buhari da ma Minista Sadiya bisa wannan tallafi da aka bayar.

A kwanakin baya ne aka samu ambaliyar ruwa a garin Keffi sakamakon ruwan sama mai ƙarfi da aka samu, lamarin da ya yi sanadiyar hasarar rayuka da dukiyoyi masu yawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *