Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Tarayya ta saki wasu kuɗaɗe don biyan albashin da ake bin ta na mambobin ƙungiyar ma’aikatan jami’o’i (NASU) da kuma na ma’aikatan da suka yi ritaya da ke karɓar fansho.
Daraktan yaɗa labarai na ofishin Akanta-Janar na Ƙasa, Bawa Mokwa ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa a ranar Asabar inda ya ce tuni an fara biyan mambobin na NASU.
Ya ce Gwamnatin Tarayya na cigaba da ƙoƙarin samar da walwala acikin ma’aikata da waɗanda suka yi ritaya a Nijeriya.
A ranar Litinin ne kwamitin haɗaka na ƙungiyoyin SSANU da NASU suka shiga yajin aikin sai baba ta gani kan riƙe albashin watanni huɗu da aka yi, wanda hakan ya haifar da koma baya ga harkokin jami’o’i a ƙasar.