Gwamnatin Tarayya ta sanar da 12 ga Yuni a matsayin hutun Ranar Dimukraɗiyya

Gwamnatin Tarayya ta sanar da 12 ga Yuni a matsayin hutun Ranar Dimukraɗiyya
Ministan harkokin cikin gida, Hon.Dr Olubunmi Tunji Ojo ya fitar da sanarwa yana mai cewa ” yayin da muke murnar zagoyowar ranar dimukraɗiya a tarihin ƙasar mu. Yana da kyau muyi waiwaye domin ganin yadda magabatan mu suka jajirce don ganin Najeriya ta zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya.
Ministan ya ƙara da cewa, Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana iya bakin ƙoƙarinsa don ganin kawo canji ga tattalin arziki da tsaron kasa.
Ministan yayi kira ga yan Najeriya da abokan ta da su yi alfahari da ita ganin yadda ta cigaba ta fannin dimukraɗiya.”

Leave a Reply