Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Tarayya ta bayyana rashin gamsuwarta ga yadda ƴan kwangilar gina titina suke gudanar da ayyukansu waɗanda ke haifar da koma-baya ga ci-gaban ƙasa da matsi ga al’umma.
A lokacin da ya ke jawabi yayin wata ziyarar gani da ido da ya kai a Jihar Ribas, Ministan Ayyuka, Dave Umahi ya yi alwashin ɗaukar mataki akan ƴan ƙwangilar da suka gaza cika alƙawarin da suka yi na ayyukan da aka ba su.
Umahi ya yi gargaɗin ne a wajen aikin wani ɓangare na titin Ahoada inda ya yi alƙawarin hukunta ƴan kwangilar kamfanonin Setraco da Rock Result bisa nuna rashin ƙwarewa a aiki.
Ya tuhume su ne da rashin sauri a aikin, yana mai cewa ba su mayar da hankali wajen gudanar da aikin ba duk da cewa an biya su kuɗaɗensu inda ya ce lallai zai fara ɗaukar mataki ta kan su don su zama abin buga misali a idon sauran injiniyoyi.
Ya ce zai umarci babban sakatare da ya ba su takardar tuhumar laifi don su yi bayanin yadda su ke gudanar da ayyukan nasu ba tare da cike sharuɗɗa ba.
Ya ce lamarin bai shafi Shugaban ƙasa ba tunda tuni ya ware kuɗaɗen gudanar da ayyukan, yana mai cewa jinkirin daga ƴan ƙwangila ne.
Saidai, Ministan ya kuma yaba da irin nagartar aikin da aka yi, amma matsalar ita ce jinkirin da aka samu.
Ya kuma yaba wa Shugaba Tinubu bisa ƙoƙarinsa na hidimta wa mutanen Neja-delta da ma sauran sassan ƙasar.
Ya yi kira ga ƴan kwangilar da su gaggauta kammala ayyukan da aka ba su cikin lokacin, yana mai barazanar ƙwace kwangila daga duk wanda aka samu da rashin tsare aikin da aka ba shi.