Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Tarayya ta soke aikin babbar hanyar Abuja-Kaduna-Zaria-Kano na ɓangaren Abuja-Kaduna daga hannun kamfanin Julius Berger.
Daraktan watsa labarai na Ma’aikatar Ayyuka, Mohammed Ahmed ya bayyana hakan cikin wata takarda da ya fitar inda ya ce hakan ya faru ne sakamakon ƙin bada haɗin-kai da kamfanin ya yi a yayin wata ganawa da gwamnati wadda ta ce za ta bada Naira biliyan 740 ga aikin wanda kamfanin ya ƙi amincewa.
An yi hukuncin ne bayan tsawon lokaci da aka ɗauka ba tare da samun wani ci-gaba ba a yayin aikin daga kamfanin.
A shekarar 2018 ne aka bai wa Julius Berger aikin akan kuɗi Naira biliyan 155.7 da cewa zai kammala a cikin shekaru uku, wanda daga bisani kuɗin aikin ya haura zuwa biliyan N600.
Bayan shekaru shida da haka ne, kamfanin ya gaza yin koda kashi 50 na aikin wanda a tsawon shekara guda kenan da Ma’aikatar ke bibiyar sa don cimma matsaya game da sauyin farashin, amma babu wani haske da aka samu.
A watan Satumba ne Majalisar Zartarwa (FEC) ta amince da da bada biliyan N740 ga kamfanin akan biliyan N797 da ya buƙata wanda aka kai a ranar 3 ga watan Oktoba.
A ranar 23 ga watan Oktoban ne Ma’aikatar ta bai wa kamfanin wa’adin mako guda na ya karɓa akan hakan ko kuma a soke kwantiragin daga gare shi.