Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da labarin ɓullar cutar tsuntsaye da ake kira da ‘bird flu’ a Jihar Kano.
Cutar, wadda ta shafi nau’ukan tsuntsaye da dama da suka haɗa da kaji da agwagi da makamantansu, ta sanya al’umma cikin damuwa game da yiwuwar yaɗuwarta a shiyyar arewa.
A cikin wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Dakta Taiwo Olasoju a madadin shugaban likitocin dabbobi ta ƙasa, hukumomi sun yi hasashen yiwuwar yaɗuwar cutar a yanayin sanyi da ake ciki.
Shugaban ƙungiyar masu kiwon kaji ta Nijeriya (PAN) reshen jihar Kano, Dakta Usman Gwarzo, ya bayyana yadda al’amarin ya fara inda aka samu batun tsirowarsa a watan Disambar da ta gabata.
Ya ce wani mutum daga Ƙaramar Hukumar Gwale ya sayi agwagwa a kasuwar Janguza, inda ya haɗa ta da gidan kajinsa, wadda ba a jima ba ta mutu, sannan daga bisani kajin baki ɗaya suka mutu.
Bayan kai su asibitin dabbobi dake Gwale, sai aka zargi cewa cutar ce ta yi sanadiyyar mutuwarsu wanda daga bisani aka tabbatar bayan bincike da likitocin suka gudanar.
Haka kuma saƙon ya yi kira ga masu kiwon kaji da su kula da wuraren kiwonsu tare ƙoƙarin ɗaukar matakan da suka dace da aiko da rahoton duk wani abin zargi ga likitocin dabbobi mafi kusa don dakatar da yaɗuwarta.