Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ce za a gyara wutar lantarkin da ta lalace a jihohi 17 na Arewacin Nijeriya sakamakon tsaiko da aka samu a tashar lantarki na Shiroro-Kaduna.
Ministan Wutar lantarki, Adebayo Adelabu ya bada tabbacin hakan wa manema labarai jim-kaɗan bayan ganawa da Shugaba Tinubu a Fadar shugaban ƙasa.
Ya ce an samu ɗaukewar lantarki ne Arewa sakamakon lalacewa da tashar ta Shiroro-Kaduna ta yi wadda ita ce babbar tashar da ke samar wa yankin wutar lantarki.
Adelabu ya ce za a ɗauki tsawon kwanaki uku zuwa biyar ana gyara ta don al’umma su cigaba da gudanar da harkokinsu cikin walwala.
Ministan ya kuma ce, tuni shugaban ƙasa ya umarci Mai ba shi shawara kan harkar tsaro (NSA) Malam Nuhu Ribaɗu da ya samar da isasshen tsaro ga jami’an da ke ƙoƙarin shawo kan matsalar lantarkin.
Ya kuma nuna damuwarsa game da lamarin a inda ya ke kira da al’ummar Arewa da su kasance masu haƙuri yayin da ake cigaba da ƙoƙarin kammala aikin.
Ya ƙara da cewa, ana kammala gyaran, ƴan Arewa za su mori lantarki fiye da yadda aka saba a baya.