Gwamnatin Tarayya za ta ɗage Shirin Ƙidayar Al’umma zuwa Mayu

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Q’Ƙidaya ta Ƙasa (NPC), ta ce ɗage zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi da aka yi zai shafi Aikin Ƙidayar Jama’a na 2023.

Idan za a iya tunawa, NPC ta shirya gudanar da aikin ƙidayar daga ranar 29 ga Maris zuwa Afrilu bayan shafe shekaru 17.

Wata majiya daga hukumar wadda ta buƙaci a sakaya sunanta, ta ce har yanzu dai hukumar ba ta yi matsaya ba amma ana kyautata zaton yanzu aikin ƙidayar zai gudana ne tsakanin 3 zuwa 7 ga watan Mayu mai zuwa.

“Shirin ƙidayar zai gudana ne daga 3 zuwa 7 ga Mayu, kuma an riga an miƙa shawarar hakan ga Shugaban Ƙasa domin amincewarsa.”

Tun da farko jaridar News Point Nigeria ta rawaito Shugaban hukumar, Nasir Isa Kwarra, ya ƙyanƙyasa yiwuwar ɗage aikin ƙidayar yayin da yake karɓar kayan aiki daga Asusun Kula da Yawan Al’umma na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNPFA) ran Alhamis Abuja.

Da yake bayani, Kwarra ya ce ba a rigada an yanke matsaya ko ba, amma Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ne zai yanke mataki na gaba da ya kamata a ɗauka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *