Gwamnatin Tarayya za ta buɗe kasuwar gwal a Kano

Daga AMINA YUSUF ALI

Gwamnatin Tarayya ta yi alƙawarin cewa, nan da watanni 10 masu zuwa za ta kammala gini sannan kuma ta buɗe kasuwar gwal ɗin da take ginawa a Jihar Kano. 

Ministan tama da ƙarafa na tarayyar Nijeriya, Arc Olamilekan Adegbite, shi ya tabbatar da haka a yayin wata ziyarar rangadi da ya kai ga kasuwar da ake ginawa a halin yanzu a jihar Kano. 

Waɗannan jawabai suna ƙunshe ne a cikin wata takarda da kakakin Ma’aikatar tama da ƙarafa, Idowu Jokpeyibo ya wallafa.

A cikin jawabin, an bayyana cewa, Shugaba Buhari na Nijeriya ya yi alƙawarin cewa, tabbas gwamnatinsa za ta kammala ginin kasuwar gwal ɗin wanda a halin yanzu ake kan aikin sa, kafin nan kafin ƙarshen shekarar da muke ciki.

Ministan tama da ƙarafa Arc Olamilekan Adegbite na Nijeriya shi ya bayyana haka a yayin ziyarar rangadi a kasuwar da ake ginawa a Kano.

Ministan ya ƙara da cewa: Wannan wani yunƙuri ne daga ɓangaren gwamnati mai ci, domin ganin an bunƙasa harkar haƙowa tare da hada-hadar duwatsu (masu daraja) domin samar da abin yi a dukkan yankuna guda 6 da muke da su a ƙasar nan. Inda ya bayyana cewa: “Wannan kasuwar Gwal da ake ginawa a ƙaramar hukumar Kumbotso, idan har aka samu nasarar kammala ta, to za ta goga kafaɗu da sauran kasuwannin gwal da suke a faɗin Duniya. 

A cewar sa, babban maƙasudin gina kasuwar shi ne, domin a samu damar sarrafa tarin gwal ɗin da Nijeriya take da shi a ƙasar, sannan a samar da ayyukan yi, kuma a samar da kuɗin shiga ga Gwamnatin. Da a ce ana ɗaukar gwal ɗin Nijeriya don sarrafawa a wata ƙasa, to gara a ce a ƙasar ma an samar da wajen sarrafa shi a ƙasar, inji shi.  

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *