Gwamnatin Tarayya za ta gurfanar da manhajojin ba da rance

Daga AMINA YUSUF ALI

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, za ta gurfanar da kamfanonin da suke tafiyar da manhajojin ba da rance a yanar gizo saboda laifin tozarta bayanan sirri na al’umma.

Hukumomin EFCC da  NITDA da kuma FCCPC suka bayyana cewa, a shirye suke don gurfanar da manyan kamfanonin rance kamar NowCash da Sokoloan da kuma 9credit saboda zargin suna fallasar da sirrikan mutane a yanar gizo. 

Wannan jawabi yana ƙunshe ne a cikin wani jawabin manema labarai da hukumar fasahar samar da bayanai ta ƙasa, NITDA ta wallafa a shafinta na Fesbuk. 

Hukumar ta bayyana cewa, a yanzu haka tana da ƙararraki na aƙalla sama da mutane 40 waɗanda suke kuka da yadda kamfanonin ba da rancen suka fallasar da bayanan sirrinsu. 

A ƙoƙarinta na daƙile yawan afkuwar fallasar da sirrikan mutane da kamfanonin rancen suke yi, hukumar ta NITDA ta haɗa gwiwa da hukumar kiyaye cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa da hukumar kare haƙƙin masu saye, (FCCPC) domin a ƙara jaddada dokar Nijeriya a game da kare haƙƙin masu saye. 

Ita dai hukumar NITDA ta gano cewa, waɗancan kamfanoni suna amfani da bayanan sirrin da al’umma suka turo musu yayin da suke ƙoƙarin amsar rancen kuɗi. Inda suke fallasar da bayanan ga wasu mutane daban waɗanda suke amfani da bayanan domin damfarar al’umma. 

Hukumar ta ce za ta tashi tsaye domin daƙile wannan matsala da ta jefa ahali da yawa a cikin ƙangin rayuwa. Har wasu ma da dama da aka damfara suna ikirarin kashe kansu saboda takaici. 

NITDA ta ce a yanzu haka sun haɗa kai da FCCPC don ɗaukar tsauraran matakai a kan duk wani kamfani da aka kama da sake yin wancan ha’inci. 

Inda a yanzu haka ma an gurfanar da kamfanin rance na Soko Lending Company. Inda aka ci shi tarar Naira miliyan goma da sauran laifuffuka. 

Daga ƙarshe, hukumar ta yi kira ga kamfanonin ba da rancen a kan su yi karatun ta nutsu domin za ta hukunta duk wanda ya yi kunnen ƙashi da wannan kashedi da ta yi.