Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima ya tabbatar da cewa gwamnatin Tinubu ta ci gaba da jajircewa wajen ƙara bunƙasa dimokuraɗiyya a ƙasar nan, inda ya bayyana cewa dole ne dukkan ‘yan Nijeriya su haɗa kai don raya dimokuraɗiyyar ƙasa.
Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima ya bayyana haka ne a ranar Talata a lokacin da ya karɓi baƙuncin wasu shugabannin ƙungiyar masu bada shawara ta jam’iyyu (IPAC) a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
A cewar mataimakin shugaban ƙasar, “Namu ƙasa ce ta matasa, tsarin dimokuraɗiyya na matasa kuma dole ne a samu fahimtar juna, fahimtar dunƙulewar dukkanin sassan da ke cikin tarayya. Kyakkyawar dimokuraɗiyya ita ce ta haɗa kai, bayar da karɓuwa kuma don haka gwamnatin Tinubu ta himmatu wajen havaka dimokaraɗiyyarmu.”
Yayin da yake zantawa da tawagar ƙarƙashin jagorancin shugaban IPAC na ƙasa, Engr. Yahaya Sani, Shettima ya yaba da rawar da IPAC ta taka wajen ganin an samu kwanciyar hankali a harkokin siyasa.
Shettima ya ce “IPAC ta cancanci yabo, muna daraja ku, IPAC tana ci gaba da dimokuraɗiyyarmu, kun cancanci yabo. A gaskiya, zan yi ƙoƙari don haɓakawa da ƙarfafa wannan dangantaka tare da cikakken tabbaci da goyon bayan shugaban ƙasa.
Mataimakin shugaban ƙasar ya shaida wa tawagar cewa duk da cewa qasar na fama da wasu ƙalubale a halin yanzu, yana da ƙwarin gwiwa ganin cewa idan aka yi la’akari da manufofi da shawarwarin da sabuwar gwamnatin ta ɗauka, lokaci ne da ba da jimawa ba ƙasar za ta shawo kan waɗannan matsaloli, ƙalubalen tattalin arziki, musamman waɗanda suka shafi cire tallafin man fetur.
Ya ce shugaban ƙasar na da matuƙar jinƙai da kuma tausayawa ‘yan Nijeriya. “A cikin watanni masu zuwa tattalin arzikin ƙasar zai daidaita kuma ‘yan Nijeriya za su fahimci manufofin gwamnatin Tinubu. Gwamnati na da ƙwaƙƙwaran tsari don magance waɗannan ƙalubalen tattalin arziki da ƙasar ke fuskanta a halin yanzu.”
Tun da farko a jawabinsa, Engr. Yahaya Sani ya taya gwamnatin Tinubu murnar ƙaddamar da ita tare da bayyana shirin IPAC na marawa sabuwar gwamnati baya domin ciyar da ƙasa gaba. Ya ce IPAC na haɗin kan ƙasa ne, haɗa kai da tattaunawa, ya ƙara da cewa akwai buƙatar jam’iyyun adawa su bada gudunmawa wajen ci gaban ƙasar. Ya kuma tabbatar da amincewarsa ga iyawar Shugaba Tinubu na kawo sauyi a ƙasar nan.
A cikin tawagar IPAC akwai Abba Kawo Ali, Shugaban Riƙo na Jam’iyyar NNPP na Ƙasa; Alhaji Shehu Masa Gabam, Shugaban SDP; Sylvester Ezeokenwa, Shugaban APGA na Ƙasa; Cif Ralph Okey Nwosu, Shugaban ADC na Ƙasa; Barr. Okechukwu Osuoha, mataimakin mai bada shawara kan harkokin shari’a a PDP; Hajiya Zainab Ibrahim, Mataimakiyar Sakatare Janar na APC, da dai sauransu.