Gwamnatin Tinubu ta yi alƙawarin haɓaka fannin ƙirƙira 

Daga AISHA ASAS 

Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi alƙawarin sabunta fannin ƙirƙira a ƙoƙarin ganin sunan Nijeriya ya fita a matsayin babban birnin da damfara ta yada zango.

Sabuwar Ministar Raya Al’adu da Inganta Tattalin Arziki, Hannatu Musawa ce ta yi wannan jawabi a lokacin da ta kai ziyara mafaifarta, Jihar Katsina, a ranar Alhamis ɗin da ta gabata.

Hannatu ta bayyana cewa, za a yi dukkan mai yiwa don ganin an goge ƙaurin suna da Nijeriya ta yi, na zama babbar ƙasa a duniya da ta fi yawaitar masu damfara.

“Za mu mayar da hankali wurin ganin mun sauya irin kallon da ake yi mana a ƙasashen duniya. Za mu tabbatar da tambarin da ake mana na babbar matattarar masu damfara ya zama tarihi.

“Duk da da cewa wannan ma’aikata ba zata tsaya iya inganta harkar nishaɗantarwa ba kawai, domin za mu tabbatar mun ciyar da ƙasa gaba ta fusakr al’adu, domin ƙasarmu ɗauke take da manyan al’adu mabambanta da ya kamata a ce mun inganta su,” inji ta.

Ministar ta ƙara da kira ga mutane da su ƙara haƙuri kan yanayin da ƙasa take ciki, kuma su cigaba da ba wa gwamnatin Shugaba Tinubu goyon baya don ganin an samu cigaba mai ɗorewa.

“Muna da qudurin ɗaukar ƙwararru da za mu yi aiki da su. Za mu gayyato qwararun ‘yan Nijeriya da ke zaune a ƙasashen waje, waɗanda suka ƙware a ɓangarorin da ake buƙata, don su zo su bada tasu gudunmawa ga cigaban wannan ɓangare.

Kuma za mu yi ƙoƙarin ganin mun samar da kuɗin shiga ga gwamnati, don ba wa gwamnatin Shugaba Tinubu namu gudunmawa na ciyar da ƙasa gaba.”

Musawa ta bada tabbacin zuwa sati mai zuwa za su fitar da jadawalin ayyukan da za su fara tare kuma da sanar da Nijeriya alƙiblar da ma’aikatar ta fuskanta.

Daga ƙarshe Hannatu ta gode wa ‘yan Nijeriya tare da neman kar su gaza a bayar da goyon baya ga Tinubu da mataimakinsa Kashim Shatima.

“Ina miƙa godiya ga ‘yan Nijeriya kan namijin ƙoƙarin da suke yin a dauriya da halin da qasa take ciki. Kuma Ina mai neman su ƙara ba wa Shugaba Tinubu da mataimakinsa Kashin Shatima goyon baya don ganin ƙudurinsu na ciyar da ƙasa gaba ya tabbata.

“Duk da cewa aiki ne da yake buƙatar haƙuri, domin suna da shiri mai inganci da za a ji daɗi idan aka yi haƙuri.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *