Gwamnatin Tinubu za ta fitar da ‘yan ƙasa miliyan 133 daga talauci — Sabuwar Minista

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sabuwar ministar harkokin jinƙai da yaƙi da fatara, Dr Betta Edu ta bayyana ƙudirin gwamnatin tarayya na fitar da ‘yan Nijeriya miliyan 133 daga ƙangin talauci.

Edu ta bayyana hakan ne a lokacin da ta fara aiki a ranar Litinin a Abuja tare da gudanar da taron gaggawa da manyan jami’an ma’aikatun da ke ƙarƙashin ma’aikatar.

Ta kuma tabbatar wa ‘yan Nijeriya aniyar ta na tabbatar da gaskiya da riƙon amana a zaman ta a matsayin minista.

Ta yi bayanin cewa, ma’aikatar za ta cimma burinta ta hanyoyi daban-daban da tsare-tsare da nufin fitar da miliyoyin ‘yan Nijeriya daga ƙangin talauci.

“Abin da ya fi muhimmanci shi ne, za mu ci gaba da mai da hankali wajen fitar da ‘yan Nijeriya miliyan 133 daga ƙangin talauci.

“Za mu iya cimma hakan a mataki-mataki, in dai akwai ƙwazo to babu abin da ba zai yiwu ba.

“Za kuma mu cimma wannan nasara tare da goyon baya mai ƙarfi daga mai girma shugaban ƙasa, Bola Tinubu da kowane memba na majalisar ministoci,” inji ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *