Daga USMAN KAROFI
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yaba da gagarumin ƙoƙarin rundunar sojin sama ta Najeriya (NAF) a yaƙi da ‘yan bindiga da ke addabar wasu yankunan jihar.
Rundunar ta ƙaddamar da wani farmaki ta sama kan ‘yan bindigar da suka kai hari a ƙauyukan Zurmi da Maradun, inda ta yi nasarar tarwatsa su a ƙarshen mako.
A wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ranar Lahadi a Gusau, ya bayyana ta’aziyya ga iyalan fararen hula da harin ya rutsa da su a Tungar Kara, Zurmi. Ya ce waɗanda abin ya shafa sun kasance ‘yan sa-kai na JTF da aka ɗauka ba daidai ba a matsayin ‘yan bindiga yayin da suke guduwa daga Gidan Makera, a yankin Boko na Zurmi.
Sanarwar ta ƙara jaddada cewa gwamnatin jihar na bayar da cikakken goyon baya ga sojoji domin tabbatar da ɗorewar nasarorin da aka samu wajen ragargazar ‘yan bindiga.
Haka kuma gwamnati ta ce za ta ƙara ƙaimi wajen samar da kayan aiki, raba bayanan sirri, da ƙarfafa haɗin kan al’umma domin ganin an samu zaman lafiya mai ɗorewa a dukkan sassan jihar.
Gwamnatin ta jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a harin, tare da addu’ar Allah ya jiƙansu da rahama ya kuma ba iyalansu haƙurin jure wannan rashi. Gwamna Lawal ya kuma yi kira ga jama’a da su kasance masu lura da duk wani abu mai ɗaukar hankali tare da bayar da cikakken haɗin kai ga jami’an tsaro domin a kawo ƙarshen matsalar tsaro a jihar.