Gwamnatin Zamfara ta kafa dokar taƙaita zirga-zirga a wasu sassan jihar

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Jihar Zamfara ta kafa dokar taƙaita zirga-zirga a yankunan da take iyaka da jihohin Katsina da Sakkwato a matsayin ɓangare na yaƙi da matsalolin tsaron da suka addabi ƙasar.

Dokar za ta fara aiki ne daga ƙarfe na 7:00 na dare zuwa 6:00 na safe.

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na Jihar, Manir Haidara, shi ne ya bayyana haka a ranar Talata.

Haidara ya ce dokar na daga shawarwarin da Majalisar Tsaron jihar ta bayar a wajen taronta.

A cewar Kwamishinan, “Daga yau, gwamnatin jihar ta ba da odar taƙaita zirga-zirga a yankin Yankara kan iyakar Zamfara da Katsina da kuma yankin Bimasa, kan iyakar Zamfara da Sakkwato daga ƙarfe 7:00pm zuwa 6:00am kulli yaumi.

“An ɗauki wannan mataki ne domin yaƙi da garkuwa da ake yi da matafiya a kan babbar hanyar Sokoto-Gusau-Funtua.

“Gwamnati ta yi hakan ne domin daƙile ayyukan ‘yan fashin daji na garkuwa da mutane, musanman a kan manyan hanyoyin jihar,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, ana buƙatar masu abubuwan hawa da matafiya kowa ya kiyaye wannan doka.

Yana mai cewa, an baza jami’an tsaro a yankunan da lamarin ya shafa domin tabbatar da jama’a ba su yi wa dokar karan tsaye ba.