Gwamnatin Zamfara ta tallafa wa iyalan ɗan jaridar da ya rasu a Kaduna

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau.

Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya ba da gudunmawar kayan abinci dabam-daban da kuma kuɗi da ba a bayyana adadinsu ba ga iyalan wakilin Jaridar The Sun, Mohammed Munirat Nasir, wanda Allah Ya yi wa rasuwa a ranar Litinin da ta gabata a gidansa da ke Kaduna.

Da yake gabatar da tallafin ga matar marigayin, Maryam Mohammed Munirat a madadin Gwamna a gidan marigayin da ke Kaduna a ranar Asabar, Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar, Ibrahim Magaji Dosara, ya ce, “Ina fatan in gabatar da waɗannan kayan abinci a matsayin tallafi ga dangin da ya bari”.

Matawalle ya bayyana alhinsa bisa rasuwar marigayin, tare da bayyana shi a matsayin mutum mai kyakkyawar alaƙa da gwamnatinsa da jama’ar jihar.

Matawalle ya tuno da yadda marigayin ya yi ƙoƙari wajen bayar da sahihan rahotanni bisa manufofigwamnatinsa.

A cewarsa, “Marigayin cikakken ɗan jarida ne wanda ya bada gagarumar gudunmawa wajen ci gaban Jihar Zamfara a lokacin rayuwarsa ba tare da yin wani rahoton ɓatanci ba”.

Daga nan Matawalle ya yi kira ga dangin mamacin da su kwantar da hankali da ɗaukar dangana kasancewar Allah Maɗaukakin Sarki Ya faɗa a cikin LittafinSa Mai Tsarki cewa, “Kowane rai sai ya ɗanɗani mutu.” Kana ya yi addu’ar Allah Ya bai wa marigayin gidan Aljanna.

Da take mayar da martani, matar marigayin, Maryam Mohammed, ta yi farin ciki da godiya da tallafin da Gwamnatin Matawalle ta ba su.

Tallafin da aka bayar ya ƙunshi abubuwa irin su manyan buhun shinkafa 4, kwalin Spaghett 2, kwalin makaroni 2, sai kuma man girki da burodi da ruwan sha.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *