Gwamnatin Zamfara ta yi alƙawarin kyautata rayuwar waɗanda ba ’yan asalin jihar ba

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Gwamnatin jihar Zamfara ta yi alƙawarin ci gaba da samar da yanayi mai kyau wajen ganin ta inganta rayuwar waɗanda ba ‘yan asalin jihar dake zaune a jihar domin su zauna lafiya da al’ummar da suke zaune.

Sabon mai bai wa Gwamna Bello Matawallen Maradun shawara na musamman Hon. Aliyu Ɗansadau ya bayyana haka a lokacin da ya karvi baƙuncin ƙungiyar waɗanda ba ‘yan asalin jihar ba da suka raka shi don kama aiki a ofishin sa.

Ɗansadau ya bayyana irin gudunmawar da al’ummar da ba ’yan asalin jihar suke bayarwa ta fuskar siyasa da tattalin arziki da zamantakewa a matsayin ci gaban jihar.

“Haƙiƙa gudunmawar da al’ummar da ba ‘yan asalin jihar Zamfara dake zaune a jihar ke bayarwa  ba za a iya misalta shi ba, don haka za mu yi ƙoƙarin inganta rayuwarsu a inda ya dace,” ya ce.

A cewar sa, gwamnatin jihar za ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da jin daɗin waɗanda ba ‘yan asalin jihar ba dake zaune lungu da saƙon jihar a wani ɓangare na manufofinta na karɓar baƙi.

Ya kuma yi kira ga ’yan asalin jihar ta Zamfara da waɗanda ba ’yan asalin jihar ba dake zaune a jihar da su zauna da juna a kodayaushe a cikin kwanciyar hankali ba tare da nuna son kai ko bambanci ba.
Ɗansadau ya ce, babu wani ci gaba mai ma’ana da za a samu idan babu haɗin kai tsakanin mutane a cikin kowace al’umma.

Ya kuma yi kira ga ‘yan asalin jihar da waɗanda ba ’yan asalin jihar da su guji nuna duk wani nau’i na ƙabilanci da addini don bai wa gwamnatin jihar damar samar musu ababen more rayuwa da kuma ci gaban jihar.

“Ina so in yi amfani da wannan kafar domin yin kira ga ‘yan Jihar Zamfara da waɗanda ba ‘yan asalin jihar ba dake zaune a jihar da su zauna da juna cikin kwanciyar hankali tare da nisantar duk wani abu na ƙabilanci, son zuciya da bambance m-bambancen addini don ci gaban jiharmu,” Hon. Aliyu Ɗansadau ya ce.

A nasa jawabin, shugaban ƙungiyar masu zaman kansu (ANI), reshen jihar Zamfara, Engr. Joel Thomas, ya bayyana jin daɗinsa kan naɗin sabon mai bada shawara na musamman ga Gwamnan Jihar ta Zamfara Hon. Bello Matawallen Maradun ya yi a kan hulɗar jama’a. 

Ya ce, a ƙarƙashin sa akwai ƙungiyoyin al’ummomi daban-daban sama da 14 da ke zaune a jihar ta Zamfara kuma ba su da wurin zama kamar Zamfara.

Ya yi alƙawarin ba gwamnatin jihar goyon baya a kullum daga mambobin ƙungiyarsa, yayin da ya yaba wa Gwamna Bello Mohammed Matawalle bisa kafa hukumar kula da hulɗa da jama’a, inda ya ce hakan zai taimaka wajen magance rikicin ƙabilanci a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *