Gwamnatinmu za ta cigaba da bada agaji ga waɗanda ambaliyar ruwa ya shafa – Buhari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya miqa saƙon jaje ga mutane sama da 500,000 da ambaliyar ruwa ya shafa a faɗin ƙasar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Malam Garba Shehu ya fitar, shugaban ya alƙawarta cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da bayar da taimakon gaggawa ga waɗanda iftila’in ta shafa.

Ya kuma yi kira ga ɗaiɗaikun masu hannu da shuni da ƙungiyoyi da su taimaka wa dubban mutanen da lamarin ya shafa.

Shugaba Buhari ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya tare da haɗin gwiwar gwamnatocin jihohi, za su yi aiki tare wajen rage ɓarnar da ambaliyar ta yi.

Haka kuma sanarwar ta ambato shugaban na kira ga mazauna wuraren da ka iya fuskantar ambaliya da su riƙa amfani da gargaɗin farko da hukumomi ke yi musu game da yiyuwar afkuwar ambaliyar.

An dai samu rahotonnin ambaliyar ruwa a jihohin Legas, da Yobe, da Borno, da Taraba, da Adamawa, da Edo, da Delta, da Kogi, da Neja da Jihar Filato.

Sauran sun hadar da Benuwai, da Ebonyi, da Anambara, da Bauchi, da Gombe, da Kano, da Jigawa, da Zamfara, da Kebbi, da Sakkwato, da Imo, da kuma Jihar Abia, tare da babban birnin qasar Abuja, inda lamarin ya shafi mutum 508,721, tare kuma da raba sama da mutum 73,379 da muhallansu.

Yayin da aka samu rasa rayuka 115, sannan kuma mutum 277 suka samu raunuka.

Sanarwar ta kumama ce gwamnati ta samu rahotonnin da ke cewa gidaje kusan da 37, 633 ne suka zube sakamakon ambaliyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *