Majalisar tattalin arzikin Ƙasa (NEC) ta karɓi rahotanni daga gwamnonin jihohi 36 kan batun kafa ‘yan sandan jihohi a ƙasar nan. Taron wanda mataimakin shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya jagoranta, ya samu halartar gwamnonin jihohi, mataimakan gwamna, ministoci da wasu hadiman shugaban ƙasa.
Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna ya bayyana wa manema labarai bayan taron cewa gwamnonin sun nuna goyon baya sosai ga kafa ‘yan sandan jihohi, duba da matsalolin tsaro da ke addabar jihohinsu. Sai dai majalisar ta ɗage tattaunawa kan batun zuwa watan Janairu 2024 domin samun cikakken rahoto daga ofishin NEC.
Gwamna Uba Sani ya yi bayanin cewa rashin isassun jami’an tsaro da wuraren da ba a kula da su suna ƙara ta’azzarar matsalolin tsaro a ƙasar. Ya ce kafa ‘yan sandan jihohi zai taimaka wajen magance waɗannan giɓin, musamman a jihohin da ke fama da matsaloli na musamman.
A wani ɓangare, majalisar ta amince da raba ƙarin kuɗaɗe ga gwamnatocin jihohin da ambaliyar ruwa ta shafa kwanan nan. Wannan kuɗin zai taimaka wajen tallafawa mutanen da ambaliyar ta shafa, tare da rage raɗaɗin asarar rayuka da dukiyoyi.
Haka zalika, majalisar ta amince da ware kashi 0.05% na kuɗaɗen da ba na man fetur ba domin tallafawa Hukumar Rarraba Kuɗaɗen Shiga ta Kasa (RMAFC). Gwamna Chukwuma Soludo na Jihar Anambra ya bayyana cewa matakin ya zama dole saboda ƙalubalen kuɗaɗe da hukumar ke fuskanta tare da neman majalisar dokoki ta ƙasa ta sabunta dokokin hukumar domin dacewa da halin da ake ciki.