Gwamnoni sun yi bankwana da Osinbajo a taron Majalisar Tattalin Arzikin Ƙasa na ƙarshe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Mambobin Majalisar Tattalin Arzikin Ƙasa (NEC) a jiya ranar Alhamis sun gudanar da wani taro na ban mamaki kuma na ban-kwana da gwamnati mai barin gado a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Taron ya gudana ne a ƙarƙashin Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo wanda shi ne Shugaban Majalisar.

Gwamnoni da wasu ‘yan majalisar zartaswa na tarayya sun tashi daga taron majalisar tattalin arziki na wata-wata da kalaman yabo ga Mataimakin Shugaban Ƙasa.

Da yake jawabi a madadin gwamnonin jihohi 36 kuma a ƙarƙashin Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF), Gwamna Aminu Tambuwal na Jihar Sakkwato ya yaba wa Osinbajo kan jagorancin majalisar “sosai da kyau”.

Ya ce Majalisar Tattalin Arzikin Ƙasa a ƙarƙashin jagorancin Osinbajo ta kasance mai inganci da nagarta.

“Kun gudanar da al’amuran majalisar cikin adalci da kishin ƙasa. Hukumar ta NEC ta kasance mai himma da aiki a ƙarƙashin jagorancin ku.

“Yawancin lokacin da yanayi ya buƙaci, NEC a ƙarƙashin jagorancinku ta tashi don fuskantar ƙalubalen rayuwarmu ta ƙasa har ma da matsalolin tattalin arziki.

“Saboda haka mai girma Shugaban Ƙasa da Mataimakin Shugaban Ƙasa a madadinmu, muna taya ku murna da kuka ɗaukaka, kuka yi wa al’umma abubuwan alfahari da kuma nuna kyakykyawan aiki da hidimar ƙasar nan a wannan matsayi, muna gode muku bisa jagorancin ku,  ya samar abu mai kyau ga kowannenmu ya bada gudunmawarsa ba tare da la’akari da yanayin mu daban-daban ba tare da nuna ɓangaranci ba, amma yana mai da hankali da kuma gudanar da ingantaccen tsarin majalisar tattalin arzikin.

“Na gode ƙwarai da gaske, muna kuma addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya ci gaba da yi muku jagora tare da ‘yan uwa a yayin da kuke kammala wa’adinku, kun ci gaba da zama wata kadara, abin kwatance, wurin tattarowa ga ƙasarmu, kamar yadda kuke ci gaba da yi, inganta harkokin shugabanci nagari da kuma cusa ayyukan dimokraɗiyya.

“Na gode ƙwarai, mun gode wa Allah da ya ba ku damar sauke nauyim da ke kanku, muna addu’ar Allah Ya ci gaba da yi muku jagora yayin da kuke cika wa’adinku na Mataimakin Shugaban Tarayyar Nijeriya, Shugaban Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa.

“A madadin mu baki ɗaya, muna gode maka, muna gode wa Shugaban Ƙasa ta hanyarka da irin gudunmawar da ya yi masa musamman ma a lokutan wahala da jihohi ke fama da qalubale da dama musamman a lokacin 2016 da jihohi da dama ba sa iya biyan albashi, amma da taimakon kuɗin beli da makamantansu sun taimaka mana, jihohi daban-daban wajen sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya ba mu kowace jiha.

“Mataimakin Shugaban Ƙasa, maigirma Shugaban Ƙasa, mun gode maka, ba za mu daina gode muku ba, mun gode maka sosai,” inji shi.

Shi ma da yake jawabi, Gwamna Nasir Ahmed El-Rufai na Jihar Kaduna ya ce shekaru takwas da Osinbajo ya yi yana shugabantar Majalisar NEC ya nuna majalisar a matsayin mafi kyawu a dukkan majalisun zartaswa da kundin tsarin mulkin Nijeriya ya bayyana.

“A cikin dukkan majalisun zartaswa na tarayya, wannan aiki ne kawai bisa tsarin mulki kuma hakan ya faru ne saboda yadda mataimakin shugaban ƙasa ke jagorantar majalisar. Ina so in yaba maku da jagorancinku. Allah zai saka maka da shugabancinka a qasar nan,” inji shi.

Nan take Gwamna Badaru Abubakar na jihar Jigawa ya ce: “Dukkanmu muna da ra’ayin da Gwamna El-Rufai ya bayyana, muna godiya da haƙurin da kuka bayar da kuma fahimtarku.”

Hakazalika, Gwamna Ben Ayade na Jihar Kuros Riba ya yaba wa mataimakin shugaban ƙasar bisa halin haƙurin da yake da shi.

A martanin da ya mayar a qarshen taron, Osinbajo ya nuna jin daxinsa da wannan karimcin.

“Na gode sosai, masu girma gwamna, zan so in gode muku da waƙar “He’s a jolly good brother” na gode sosai, Ina so in gode wa Masu girma Mambobin Majalisar Tattalin Arziƙi na Ƙasa. jajircewarku da kishin qasa da kuma yadda kuka yi aiki tuƙuru don ganin ƙasarmu ba kawai gwamnatin tarayya ta bada shawarar da ta dace ba, a’a, ƙasar nan tana riƙe da ita a kowane lokaci.

“Ina ganin tuni an yaba wa muryar da ke tabbatar da zaman lafiya ta Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa, ciki har da Shugaban Ƙasa da kansa a lokuta da dama da ya samu dalilin yin tsokaci kan ayyukan Majalisar Tattalin Arzikin Ƙasa da na ku, gwamnoni.

“Majalisar Tattalin Arzikin Ƙasa ta kasance tana ba da shawarwari musamman ma tambayoyin da suka shafi tallafi, rahotanni, akwai kuma yanayin da Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa ta ba da shawara kan al’amura da dama da suka shafi tattalin arzikin ƙasar.

“Kuma shawarar ku koyaushe tana kan gaskiya, shawarar ku koyaushe tana kan gaskiya cikin maslahar ƙasa baki ɗaya.

“Dole ne in ce ta hanyoyi da dama, Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa a shekarun baya ko 10 zuwa 15 ta nuna cewa qasarmu tana da ingantaccen shugabanci, shugabancinku na siyasa ya nuna ta hanyoyi da dama, muna mutunta aiki tare a matsayinmu na ƙasa baki ɗaya.

“Dole ne in yaba muku da ganin cewa a duk shawarar da muka yanke, haɗin kan ƙasarmu ya taka muhimmiyar rawa, don haka ina ƙara gode muku da kuka yi aiki tare da mu cikin shekaru 8 ko fiye da haka, ina kuma addu’ar Allah ya taimaka, dukkan ku fiye da yadda kuke zato, Allah Maɗaukakin Sarki zai saka muku da irin gudunmawar da kuke bayarwa a jihohinku da al’ummarmu.

“Ina kuma addu’a ga waɗanda suka ci gaba, gwamnonin da suke ci gaba da masu shigowa, da cewa za ku samu mafi kyawun shekarun al’ummarmu da kuma cewa al’ummarmu da ke ƙarƙashinku, da jihohinku da ke ƙarƙashin ku, za su ci gaba da bunƙasa,” inji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *