Gwamnonin Kudu sun haramta kiwo barkatai a yankinsu, sun buƙaci a sake fasalin ƙasa

Yayin wani taro da suka gudanar a ranar Talata a Asaba babban birnin jihar Delta, gwamnonin Kudu sun yi ittifaƙi kan haramta kiwo barkatai a yankinsu.

Cim ma wannan matsaya da gwamnonin suka yi hakan ba ya rasa nasaba da matsalar tsaron da suka ce yankin nasu na fama da ita.

Kazalika, yayin taron nasu gwamnonin sun ƙalubalanci Gwamnatin Tarayya a kan ta gaggauta sake fasalin ƙasa domin magance matsalolin tsaron da ke ci gaba da cinye wa ƙasa tuwo a ƙwarya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *