Gwanjon jirgi Tinubu ya saya, ba sabo ba – Fadar shugaban ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI

Kakakin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya ce mai gidansa, Shugaba Bola Tinubu bai sayi sabon jirgi mai tashin angulu ba, a madadin haka, wanda aka yi gwanjonsa ne ya saya.

Onanuga ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin wata hira da gidan talabijin na ‘channels’, inda ya ce jirgin ba na Shugaba Tinubu bane, amma kadara ce ta ƴan Nijeriya.

Ya ce akwai jiragen da ke cikin mummunan yanayi da ba za a iya aiki da su ba wa Shugaba Tinubu saboda tsufa da suka yi da kuma tsadar kula da su da ake yi, ya na mai bada misali da wani jirgin ƙirar Boeing B737-700 mai shekaru 19 da aka saya tun zamanin tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo.

A madadin amfani da wasu maƙudan kuɗaɗen wajen gyaran jirgin sama, sai Shugaba Tinubu ya nemi amincewar Majalisa don sayen gwanjon jirgi mai kyau.

Ya ƙara da cewa, sayan jirgin zai taimaka wajen rage adadin da ake kashewa a kula da tsohon.

Mai magana da yawun shugaban ƙasar ya kuma yi kira ga al’umma da su fifita lafiyarsa, ya na mai cewa wanda aka mallaka ma nasu ne ba na Tinubu ba.