Haƙƙin shugabanni ga talakawa

Assalamu alaikum. Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa mu ke nema, kuma muna neman tsarinsa daga shirrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai ɓatar da shi, wanda kuma ya ɓatar, to babu mai shiryar da shi.

’Yan uwana Musulmi, Allah Maɗaukakin Sarki yana cewa a cikin littafinsa mai tsarki, “A yau na cika muku addininku, kuma na cika muku ni’imata gareku, na yardar muku musulunci ya zama addini gareku”. (Al-Ima’ida:3)

Haƙiƙa addinin Musulunci addini ne cikakke ta kowanne ɓangare, don haka Musulmi ba sa buƙatar wani addini wanda ba shi ba, basu buƙatar wata shari’a wadda ba ita ba, saboda cikar shari’ar musulunci, ta ƙunshi dukkan abin da ya ke maslaha ne ga al’umma, ta bawa dukkan mutane haƙƙoƙinsu, talakawa da masu arziƙi, masu mulki da waɗanda ake mulka, namiji da mace, kai har ma da dabbobi, Allah Maɗaukakin Sarki ya ba duk wani mai haƙƙi haƙƙinsa.

To daga cikin abin da Musulunci ya ba shi kulawa, al’amarin shugabanci da jagoranci, musulunci bai bar mutane su zauna kara zube ba, a’a ya yi umarni da naɗa shugaba koda a halin tafiya ne, saboda amfanin samun shugaba a cikin al’umma amfani ne bayananne baya buƙatar wani dogon bayani, don rayuwar mutane ba za ta tsayu ta gyaru ba sai idan akwai shugabanci a cikinsu, don haka Allah maɗaukakin sarki da Manzon Allah suka nuna mahimmancin bin shugaba da samun shugabancin a cikin mutane, Allah Maɗaukakin Sarki ya ce, “Ya ku waɗanda kuka yi imani ku bi Allah, ku bi Manzon Allah, (sannan ku bi) ma’abota al’amari daga cikinku” (Al – Nisa’i 59).

An karɓo daga Ummu Salama, matar Annabi, daga Annabi ya ce, “Haƙiƙa za a naɗa muku shugabanni a bayana, waɗanda za ku ga abu mai kyau a tare da su, kuma ku ga marasa kyau, wanda ya qi maras kyau ɗin ya kuɓuta, haka ma wanda ya yi inkari, sai dai wanda ya yarda ya bi (to wannan mai laifi ne). Sai sahabbai suka ce “ba za mu yaƙe su ya Manzon Allah? Sai ya ce, “a’a, matuƙar dai suna yin sallah”. Muslim ne ya rawaito shi.

Ya ’yan uwa. Waɗannan kaxan kenan daga cikin dalilan da suke nuna muhimmancin samar da shugabanci a Musulunci, saboda haka ma musulunci ya tsara haƙƙoƙin shugaba akan talakawansa, ya kuma tsara haƙƙin talaka a kan shugabansa.

Yana cikin haƙƙin talakawa akan shugabansu ya samar musu da kotunan da za su riƙa yanke hukunci tsakanin mutane da sasanta su, ya samar da kwamitocin da za su riƙa sasanta mutane, suna umarni da kyakkyawan aiki suna hana mummuna. Kamar yadda ya ke wajibi ne akan shugaba ya tsaida haddi akan duk wanda ya ƙetare iyaka, ya zalunci bayin Allah, ya tava rayukansu ko jininsu ko dukiyoyinsu, Manzon Allah yana cewa, “Haddi ɗaya da za a yi aiki da shi a bayan ƙasa, ya fi a yi wa mutanen ƙasa ruwa na kwana arba’in”.

Hakanan haƙƙi ne akan shugaba ya sadar da haƙƙoƙi ga masu su, ya samar da ’yan sanda, waɗanda za su ba da tsaro ga mutane da dukiyoyinsu, saboda rayuwa ba ta yiwu wa sai da tsaro, kamar yadda wajibi ne akan shugaba ya gina makarantu da wuraren ibada, ya samar da ƙwararrun malamai waɗanda za su koyar da al’umma addini kamar yadda Manzon Allah ya zo da shi. Ya taimaka wa masu bincike, ya taimaka a wajen buga littattafan addini da sauran irin waɗannan ayyuka.

Hakanan wajibi ne akan shugaba ya zama mai adalci tsakaninsa da talakawansa, saboda adalci shi ne tushen rayuwa, kuma da adalci ne al’amura suke daidaita duniya da lahira.

Manzon Allah yana cewa, “babu wani zunubi da ya fi sanya azaba da wuri fiye da zalunci da yanke zumunci.” Azzalumi ana buge shi a duniya koda kuwa an masa gafara da rahama a lahira, saboda adalci tsari ne a cikin komai da komai, idan aka tsayar da al’amarin duniya akan adalci sai komai ya tsaya, koda kuwa ma’abocin duniyar nan ba shi da rabo a lahira, idan kuwa ba tsayar da al’amurar duniya akan adalci ba, to lamarin ba zai tsaya ba, ko da kuwa ma’abocinsa yana da imanin da zai ishe shi a lahira.”

Haka nan shugaba ya zama ƙarfi wajen zartar da abin da yake gaskiya ne a cikin talakawansa, ya nisanci zalunci, da ƙarya da cin amana, da ha’inci, da sauran munanan halaye.

Waɗannan su ne kaɗan daga cikin haƙƙoƙin talakawa a kan shugabaninsu, don haka wajibi ne akan shugabanni su kiyaye waɗannan haƙƙoƙi, saboda al’amuran talakawansu amana ce a wuyansu, Allah zai tambaye su abin da ya ba su kiwo na daga bayinsa. Ku ji tsoron Allah ya ku shuwagabanni, ku kamanta, ku nemi taimakon Allah ta hanyar sallah da haƙuri, Allah yana tare da masu haƙuri, kuma kyakkyawan ƙarshe yana ga masu tsoron Allah.

Allah Maɗaukakin Sarki ya yi mana albarka cikin abin da muka ji na Alƙur’ani da Hadisi, haƙiƙa shi mai iko ne akan komai.

Daga MUSTAPHA MUSA MUHAMMAD, ɗalibi a fannin karatun Injiniyancin Sinadarai (Chemical Engineering) a Federal Polytechnic Kaduna, 09123302968.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *