Haƙar ma’adanai: Najeriya ta yi tayi mai maiƙo ga masu zuba jari

Daga AMINA YUSUF ALI

Gwamnatin Nijeriya ta yi kira ga al’umma da su zo su zuba jari a harkar haƙar ma’adanai a ƙasar. Inda Gwamnatin ta yi tayi maiƙo ga dukkan waɗanda za su zuba jari a harkar. Wato Gwamnatin ta ce za ta mallaka musu dukkan ma’adanan ko albarkatun ƙasar da suka haƙo ba tare da ta karɓi ko tsinke ba. Sannan za ta yafe musu haraji na tsawon lokaci. Wannan tayi ya haɗa da dukkan masu sha’awar zuba jari na gida Nijeriya da kuma na ƙasashen ƙetare. 

Ministan masana’antar tama da ƙarafa, Olamilekan Adegbite, shi ya bayyana hakan a ranar Talatar da ta wuce a Abuja. A yayin da yake jawabin ƙaratowar bikin makon haƙar ma’adanan Nijeriya, karo na shida. 

Inda Olamilekan Adegbite, ya ƙara da cewa, Gwamnatin ta yi tayin ba wa mallaka wa masu zuba jari a harkar ma’danai dukkan abinda aka haƙo tare da yafe musu harajin shekaru uku cur domin a samu a farfaɗo da masana’antar ma’adanai da a halin yanzu take masassarar mutuwa. 

A yayin zantawar sa da  ‘yan jaridu, Ministan ya bayyana cewa: “Masu haƙar ma’adanai da yawa na wasu ƙasashen Duniya ba su san cewa, Nijeriya ƙasa ce mai ma’adanai ba. Don haka mu ma muna so su shigo Nijeriya su yi harkar haƙar ma’adanan domin sai mun fi kyautata musu sama da sauran ƙasashen da suke zuwa haƙar ma’adanan.”

Ya ƙara da cewa, sam ba sa karɓar wani haraji mai yawa. Ko a da ma can abinda suke amsa a wajen masu haƙar kaso 3. 5  na ma’adanan a cikin ɗari. Yayin da sauran ƙasashen kuma suke amsar kaso 17 zuwa 20 wani kuma ya danganta da irin yawan ma’adanan da aka haƙo. 

Da wannan ya ce, yana gayyatar manyan mutane masu hannu da shuni a ciki da wajen ƙasar nan su kawo gudunmowa ta hannun jari a sashen ma’adanan ko ba don komai ba sai don samun tarin garaɓasar da take ciki. Har ma da ƙarin samun damar hada-hadar kuɗi kyauta ta Babban Bankin Nijeriya, CBN. 

Shi dai makon haƙar ma’adanai na Nijeriya  mai taken: “Ribobi bakwai tattare da zuba jari a harkar haɓar ma’adanan Nijeriya”, ana sa ran za a gudanar da shi ne, a ranakun 16 da 17 na watan Nuwamba, 2021 idan rai ya kai.

Taron wanda za a gudanar a Abuja zai haɗo kan manyan ‘yan kasuwa, gwamnoni, Ministoci, da makamantansu. Kuma ana sa ran mataimakin shugaban ƙasar Nijeriya Farfesa Yemi Osinbajo shi zai buɗe taron.