Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Nijeriya da ƙasar Cuba sun ɗauki manyan matakai na ƙarfafa alaƙar harkokin diflomasiyya da tattalin arziki domin inganta ɓangarorin lafiya, ilimi da kasuwanci.
Hakan ya kasance ne a lokacin da ƙasashen biyu suka cika shekaru 50 da ƙulla alaƙar diflomasiyya da aka fara a shekarar 1974.
Mataimakin Shugaban ƙasa, wanda ya karɓi baƙuncin Ministan Harkokin Waje na ƙasar, Rodriguez Parrilla da Jakadan ƙasar ga Nijeriya, Mariam Morales Palmeri a Fadar Shugaban ƙasa a Abuja, ya bayyana Cuba a matsayin ƙasaitacciyar ƙasar da ka iya nasara a kowane irin ci-gaba.
Ya ce, duk da cewa ƙasar a Kudancin Nahiyar Amurka ta ke, amma zuciyarta ta na Afirka ganin yadda ta ke taka muhimmiyar rawa ga harkokin walwala da jin daɗin al’umma da ƙasashensu.
Ya kuma ce, akwai da dama daga ’yan ƙasar da ke da asali a Afirka musamman a Nijeriya, wadda galibin waɗanda suka yi nasara a rayuwa ke alfahari da ita.
Shettima ya tabbatar wa wakilan ƙasar cewa Nijeriya za ta cigaba da martaba ƙoƙarinta da nemana hanyoyin da za su ƙarfafa alaƙa, musamman a ɓangaren lafiya da ci gaban riga-kafi.
A nasa jawabin, Minista Bruno Rodriguez ya bayyana alaƙar ƙasashen a matsayin abinda aka jure a kai, wanda a sakamakon haka an cimma nasarori da dama tun tsawon shekaru 50 da farawa, ya na mai yaba wa gudunmawa da ’yan Afrika ke bayarwa ga ci gaban ƙasar Cuba.
Rodriguez ya ce, ba don tallafawa na ’yan Afirka da Nijeriya ba, da zai yi wuya su kai matsayin da suke a yanzu, wanda ya samu ne sakamakon warware ɓarakar da ke tsakanin su da girmama juna.