Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Babban Hafsan Rundunar Sojin Saman Nijeriya, Air Marshal Hasan Abubakar, ya jajenta wa iyalan jami’an jirgin da suka mutu na jirgin sama mai saukar ungulu ƙirar MI-171E da ya yi haɗari a Jihar Neja a ranar 14 ga watan Agustan 2023.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da rundunar sojin saman Nijeriya, Daraktan hulɗa da jama’a da yaɗa labarai, Air Commodore Edward Gabkwet ya fitar.
Da yake jajantawa iyalan, Air Marshal Abubakar ya bayyana cewa, wannan rashin babban koma baya ne ga rundunar sojin saman Nijeriya, wanda zai ɗauki tsawon lokaci kafin hukumar ta farfaɗo.
Ya kuma tabbatar wa da iyalan cewa NAF ba za ta yi watsi da su ba.
“Hukumar NAF za ta kasance tare da ku a koyaushe kuma za ta ba ku goyon baya har zuwa ƙarshe”, tare da tabbatar musu da cewa sadaukarwar da suka yi ba za ta faɗi ƙasa banza ba kamar yadda NAF da kuma duk ‘yan Nijeriya za su riƙa tunawa da su har abada don sadaukar da rayukansu don rayuwar al’ummar ƙasar.
Air Marshal Abubakar ya kuma yi amfani da damar ziyarar wajen ganawa da jami’ai da ma’aikatan sashen.
A yayin zaman tattaunawa, shugaban ya jajantawa sashen tare da yaba musu bisa jajircewa da ƙoƙarin da suke yi a ayyukan haɗin gwiwa na rundunar soji a yankin Neja Delta.
Ya kuma ba su tabbacin cewa sadaukarwar da jaruman da suka mutu ba za su kasance a banza ba, kuma rundunar sojojin saman Nijeriya za ta yi duk mai yiwuwa don daƙile afkuwar hakan a nan gaba.
Idan dai za a iya tunawa, wani jirgin saman NAF MI-171E da ke aikin kwashe mutanen da suka mutu ya yi hatsari a jihar Neja a ranar 14 ga watan Agustan 2023, inda ya kashe fasinjojin baki ɗaya da jami’an NAF 4 da ke cikin jirgin.
Ma’aikatan jirgin da suka mutu sun haɗa da Laftanar Adamu Ibrahim, Laftanar Anthony Duryumus, Lance Kofur Alaribe Daniel da Lance Kofur Briggs Stephen Peter.
Jami’an runduna biyu na NAF, Kofur Jauro Amos da Lance Kofur Abdulrahman Abubakar suma sun rasa rayukansu a wani vangare na sojojin Nijeriya da ’yan ta’adda suka yi wa kwanton vauna a Jihar Neja kwanan nan.