Haɗarin matakin Amurka na sayar wa Taiwan makamai

Daga SAMINU HASSAN

Masharhanta da dama na ci gaba da ganin baiken alaƙa, da cuɗanyar dake wakana tsakanin Amurka da yankin Taiwan na ƙasar Sin, inda sau da dama, Amurka ke sayarwa yankin na Taiwan makaman aikin soji, matakin da ya yi matuƙar sabawa dokokin ƙasa da kasa, da ƙa’idojin da ƙasashen duniya suka amincewa, da yarjejeniyoyin da ita kanta Amurka ta ƙulla tare da ɓangaren ƙasar Sin.

A lokuta mabanbanta, Sin ta sha nuna rashin amincewarta da waɗannan matakai na tsoma hannu cikin harkokin gidan ta, matakin da ka iya haifar da yanayi na rashin jituwa tsakanin Sin da Amurka, da gurgunta alaƙar sassan biyu, tare da haifar da zaman ɗar ɗar a zirin Taiwan.

Ko da a baya bayan nan ma, wasu rahotanni sun nuna yadda Amurka ta sanya hannu kan wasu kwangiloli na sayarwa Taiwan wasu na’urorin sadarwa na aikin soji, waɗanda kuɗin su ya kai kimanin dalar Amurka miliyan 245. An kuma bayyana cewa, yankin na Taiwan zai karɓi na’urorin a watan Satumbar 2025, a wani ɓangare na zartas da shirin Amurkar na sayarwa Taiwan makamai da sassan suka amincewa tun a watan Disambar shekarar 2020.

Ko shakka babu, abu ne mai ban mamaki, yadda sau da yawa Amurka ke bayyana amincewarta da manufofin ƙasar Sin, na kasancewar Sin ɗaya tak a duniya, kuma ƙasa mai ikon mulkin kai da dukkanin yankunanta. A hannu guda kuma, take aiwatar da irin waɗannan matakai na sayarwa Taiwan da makamai ta bayan fage.

Hakan tamkar tufka da warwara ne. Kuma mataki ne mai haɗarin gaske, wanda zai haifar da babbar baraka tsakanin Amurka da Sin, zai kuma ci gaba da zubarwa Amurka da kima a idanun duniya, duba da matsayinta na babbar ƙasa mai fada a ji, amma kuma a lokaci guda, mai saɓa alƙawuran da ta dauka, tare da rura wutar sabani, da rikici, da ta da zaune tsaye!