Haɗarin mota ya ci mutum 5 a Neja

Daga BASHIR ISAH

An samu aukuwar mummunan haɗari a safiyar Alhamis a babbar hanyar Lambata zuwa Kwakuti da ke yankin ƙaramar hukumar Gurara a jihar Neja wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutum 5 da jikkata mutum 3.

Wasu da lamarin ya auku a gabansu sun bayyana cewa, haɗarin ya auku ne sakamakon taho-mu-gama da aka yi tsakanin wata Golf 3 mai lamba KTU 506BK da kuma Salon Mazda 326 mai fenti ruwan ɗorawa, wanda duka motocin biyu na kasuwa ne.

Kazalika, sun ce haɗari na da nasaba da ruwan saman da aka samu a yankin da kuma yadda motocin suke gudun wuce sa’a.

An ga jami’an kiyaye haɗurra (FRSC) a inda haɗarin ya auku inda suka yi hidimar jigilar waɗanda hadarin ya rutsa da su zuwa asibiti mafi kusa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *