Haɗarin yaɗa ƙabilanci

Tsohon Shugaban Ƙasar Nijeriya, Cif Olusegun Obasanjo, ya yi Allah-wadai da ƙabilanci da kuma barazanar da ’yan ƙabilar Ibo ke fuskanta kafin zaɓen 2023 da kuma bayan kammala zaɓen 2023 a Legas. Dattijon wanda ya yi magana a ranar Asabar a Awka a yayin bikin cika shekara guda a kan karagar mulki na Gwamna Chukwuma Charles Soludo na jihar Anambra, ya yi gargaɗi kan kyamar ƙabilar Ibo, ya kuma buƙaci ɗaukacin ’yan Nijeriya da su zauna lafiya da juna.

Hakazalika, ƙungiyar ƙoli ta al’adun ƙabilar Ibo ‘Ohanaeze Ndigbo Worldwide’, ta yi tir da hare-haren ba gaira ba dalili da aka kai wa ’yan ƙabilar Ibo mazauna Legas kafin da lokacin da kuma bayan zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu da kuma zaɓen gwamnoni da na ’yan majalisar jiha na ranar 18 ga Maris. Hare-haren da ba su dace ba, a cewar sakataren yaɗa labaran ƙungiyar na ƙasa, Dr Alex Ogbonnia, sun haɗa da rashin tausayi, danniya, da kuma barazana ga ƙabilar Ibo.

Ƙungiyar Ohanaeze Ndigbo ta kuma yi Allah wadai da zage-zagen ƙabilanci da Bayo Onanuga, mai magana da yawun zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu, da Musiliu Akinsanya, shugaban kwamitin kula da wuraren shaƙatawa na jihar Legas, wanda aka fi sani da MC Oluomo da wasu ’yan ƙabilanci suka yi. Ƙungiyar ta bayyana cewa, “A yayin da ake tunkarar zaɓen shugaban ƙasa a ranar 25 ga Fabrairu, 2023, Ndigbo a Legas ya fuskanci cin zarafi daga waɗanda ake kira ‘masu Legas’, wanda hakan ya sa aka riƙa kai wa da yawa daga cikin mutanenmu hari, an zalunce su, an danne su, da kuma hana su damarsu ba don wani dalili ba face nacewa a kan ’yancinsu na ’yan ƙasa na zaɓen ’yan takarar da suke so.”

Sai dai kuma zaɓaɓɓen shugaban aasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya kuma yi tir da zagon ƙasa, kalaman ƙabilanci da tashe-tashen hankula da suka biyo bayan zaɓen 2023, ya kuma buƙaci da a fara shirin neman waraka tun da zave ya ƙare. Ko da yake Tinubu ya yi jinkiri, ya kamata ya kira mataimakansa da masu goyon bayansa don samun tsari. Wasu ’yan Najeriya sun bayyana kalamai da barazanar da ’yan ƙabilar Ibo ke fustanta a Legas a matsayin maras tushe kuma ba su dace ba.

Mun kyamaci aaruwar ƙabilanci a jihar Legas sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisar tarayya. Idan ba a daina wannan ɗabi’a ba, to hakan zai kawo cikas ga dimokuraɗiyyarmu da kuma makomar ƙasar nan. Harin da aka kai wa ƙabilar Ibo a Legas hari ne ga ɗaukacin Nijeriya da kuma cigaba da zama tare. Abin baain ciki shi ne, ƙarar ƙabilanci ya ƙara fallasa bambance-bambancen da ke tsakaninmu da kuma kokwanton bambancinmu da haɗin kai.

Kafin lokacin zaɓe, ’yan aabilar Ibo da ke zaune a yankin Eti-Osa a jihar Legas, sun yi zargin cewa shugaban ƙaramar hukumar ya gayyaci ’yan jam’iyyar APC tare da yi wa Ibo barazanar cewa za su kaɗa wa jam’iyyar APC ƙuri’a ko kuma su fuskanci abin da zai biyo baya. A Ije-Ododo na ƙaramar hukumar Ojo, an yi irin wannan barazana ga Ibo. A Oshodi, MC Oluomo ya yi barazana ga duk wani ɗan ƙabilar Ibo da zai yi yunƙurin zaɓen wata jam’iyya ba APC ba. Sakamakon haka, wasu da ake zargin ’yan daba ne suka lalata kasuwanni da wuraren kasuwanci na ’yan ƙabilar Ibo a wasu sassan jihar.

Bayan zaɓen gwamna na ranar 18 ga watan Maris, Onanuga ya gargaɗi aabilar Ibo da su daina tsoma baki a harkokin siyasar Legas. Ya ce, “shekarar 2023 za ta kasance lokaci na ƙarshe na tsoma bakin ‘yan ƙabilar Ibo a siyasar Legas. Kada a sake a 2027. Legas ba kamar Anambra ba ce, Imo ko kowace jiha a Nijeriya. Ba jihar mutum ba ce, ba Babban Birnin Tarayya ba ce. Ƙasar Yarbawa ce. Ku yi hankali da kasuwancinku.” Har ma ya yi taƙama da cewa ba shi da uzuri kan zagin ƙabilanci da ake yi wa ƙabilar Ibo.

Bambance-bambancen ƙabilanci ba daidai ba ne kuma ya saɓa wa zaman tare cikin jituwa a cikin ƙasa kamar Nijeriya. Kisan kiyashin da aka yi a ƙasar Rwanda a shekarar 1994, wanda ya yi sanadin mutuwar ‘yan ƙabilar Tutsi kusan miliyan ɗaya da sauransu, na nuni da haɗarin da ke tattare da ƙabilanci. Babu shakka, kalaman izgili da ƙiyayyar ƙabilanci sun taimaka sosai ga rikicin siyasa na 1966 da kuma yaqin basasar Nijeriya na 1967-1970, wanda ya ci rayuka sama da miliyan uku.

Don haka ya kamata ’yan siyasa su hana mataimakansu da magoya bayansu yin kalamai masu zafi da za su iya jefa ƙasar nan cikin wani rikicin da za a iya kaucewa. Kalaman kyama da hargitsin ƙabilanci na iya haifar da rikicin ƙabilanci da yaƙe-yaƙe. Baya ga rarrabuwar kawuna, ba su dace da dokokin ƙasa ba waɗanda suka tabbatar da haƙƙin kowane ɗan Nijeriya ba. ’Yan siyasa da magoya bayansu su yi la’akari da kalamansu na ɓangaranci. Abin takaicin da ya faru a Legas abin la’akari ne matuƙa.

Abin baƙin ciki shi ne, jami’an tsaro ba su kama waɗanda ke da irin wannan ra’ayi ko barazana ba. Har yanzu bai makara ba ’yan sanda da sauran jami’an tsaro da abin ya shafa su kama tare da yi wa waɗanda suka yi wa wasu ’yan Nijeriya barazana da kuma hana su haƙƙoƙinsu a zaɓen 2023 a Legas da sauran jihohin ƙasar. Don fara tabbatar da adalici a Nijeriya.

Dole ne a gurfanar da waɗanda suka yi wa wasu ’yan Nijeriya barazana tare da ƙona kasuwanninsu a gaban kuliya. Makomar Nijeriya za ta iya lalacewa ba tare da adalci da daidaito ga dukkan ’yan ƙasa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *