Haɗarin jirgin sama ya ci rai 7 a Abuja

Daga AISHA ASAS

Wani jirgin sama mallakar Rundunar Sojin Saman Nijeriya, mai lamba NAF 201 B350, ya yi haɗari a Abuja.

Bayanai sun nuna lamarin ya faru ne da hantsin Lahadi bayan da jirgin ya samu matsalar inji inda ya yi haɗari garin sauka a Abuja.

Sanarwar da ta fito daga Jami’in Haulɗa da Jama’a na Rundunar, Air Commodore Ibikunle Daramola, ta nuna tuni shugaban rundunar Air Vice Marshal IO Amao, ya bada umarnin gudanar da bincike kan lamarin.

Baya ga tabbatar da aukuwar lamarin, Daramola ya sake tabbatar da cewa duka mutum 7 da ke cikin jirgin sun riga mu gidan gaskiya.

Shugaban rundunar ya buƙaci jama’a kowa ya kwantar da hankalinsa sannan a jira sakamakon binciken da za a gudanar.

Daga nan, ya yi amfani da wannan dama wajen jajanta wa iyalan waɗanda haɗarin ya rutsa da su.