Haɗin gwiwar Afirka da Sin a fannin kare muhalli zai haifar da ɗa mai ido

Daga CMG HAUSA

Ranar 10 ga watan Afrilu, ita ce ranar kare muhalli ta nahiyar Afirka. Haƙiƙa kare muhalli wani muhimmin ɓangare ne da ke tabbatar da ɗorewar ci gaban tattalin arziki, da kyautatuwar zaman rayuwar jama’a.

Birnin da nake zama a ciki, wato Beijing na ƙasar Sin, ya taɓa fama da matsalar guguwar rairayi sosai, inda a duk shekara a kan samu wasu kwanaki da iska mai ƙarfi, ɗauke da rairayi ke hana mutane fitowa daga gidajensu. Amma daga bisani, ta hanyar daddasa itatuwa bisa shiri, an kawar da wannan matsala, ta yadda mutane suka samu ƙarin damammakin bulaguro a lokacin bazara.

Sa’an nan a ƙauye na dake kudancin ƙasar, wata ma’aikatar sarrafa takardu, ta fitar da ruwa mai guba cikin koguna, lamarin da ya haddasa gurbacewar ruwa.

Sai dai zuwa yanzu, albarkacin manufar inganta masana’antu, an riga an rufe ma’aikatar. Ta yadda kogunan wurin suka sake zama gidajen kifaye, da wurin wasa na yara. Waɗannan abubuwa sun shaida cewa, kyautatar muhalli za ta haifar da ingancin zaman rayuwar jama’a.

Fasahohin da ƙasar Sin ta samu, wajen kare muhalli, za a iya yin amfani da su a ƙasashen Afirka. A cikin hamadar Taklamakan dake arewa maso yammacin ƙasar Sin, akwai wasu hanyoyin mota 4, waɗanda ko wacensu tsawonta ya kai kimanin kilomita 500. Don magance rairayi ya binne hanyoyin, ƙwararru masu nazarin kimiya da fasaha na ƙasar Sin, sun tsara fasahohi daban daban, ta yadda suka dasa dimbin itatuwa, da ciyayi masu jure fari a gefunan hanyoyin.

Haka kuma, ana ta ƙoƙarin haɓaka itatuwan, da ciyayin cikin shekarun da suka gabata. Ta haka, an kai ga kare hanyoyin, gami da kyautata muhallin hamadar.

Zuwa yanzu, ana yin amfani da waɗannan fasahohi na ƙasar Sin, wajen gina wata “babbar ganuwa mai launin kore” a nahiyar Afirka. An ƙaddamar da aikin a shekarar 2008, inda ake neman samar da wani ziri na itatuwa da ciyayi, wanda zai haɗa Senegal dake yammacin Afirka, da Djibouti dake gabashin nahiyar. Ta wannan ziri na musamman, ana fatan hana haɓakar hamadar Sahara, da kyautata muhallin yankin Sahel dake nahiyar Afirka.

Ban da daƙile kwararar hamada, ƙasashen Afirka da kasar Sin suna hadin kai da juna sosai, ta fuskar samar da makamashi mai tsabta. A watan Maris da ya gabata, madatsar ruwa ta Zungeru, wadda ita ce mafi girma a tarayyar Najeriya ta fara samar da wutar lantarki.

Wannan tashar da wani kamfanin ƙasar Sin ya gina a kan kogin Kaduna, za ta iya samar da wutar lantarki mai tsabta har KWH biliyan 2.64 a duk shekara. Ban da wannan kuma, kasar Sin ta taimakawa ƙasar Afirka ta Kudu, wajen gina tashar samar da wutar lantarki ta ƙarfin iska ta De Aar, da gina tashar wutar lantarki ta hasken rana a Garissa na ƙasar Kenya.

Idan an kwatanta da kyautata fasahohi, sabunta tunanin mutane ya fi muhimmanci. Yanzu haka Sinawa sun samu tunani na raya ƙasa ta hanyoyi masu kare muhalli, waɗanda za su dore, sa’an nan suna baza wannan tunani a ƙasashen Afirka. Misali, a jihar Benue ta Najeriya, wani kamfanin Sin ya kafa wata ma’aikatar haɗa sinadarin sifirit ta rogo.

Inda dukkan ruwan da ma’aikatar ke fitarwa ake tace shi don tabbatar da tsabtarsa, kana sauran shara ana sarrafa ta zuwa taki da iskar gas. Babu gurɓacewar muhalli, kuma babu salwantar da albarkatu, waɗanda suka kasance ainihiyar ma’anar “samun ci gaba mai ɗorewa da kare muhalli”.

Wajen taron ministoci karon 8 na dandalin haɗin gwiwar Sin da Afirka, da ya gudana bara, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya sanar da manyan ayyukan guda 9 game da haɗin kan Sin da Afirka, ciki har da aiki na samun ci gaba ba tare da gurɓata muhalli ba. Dalilin da ya sa ƙasar Sin ke dora muhimmanci ga wannan ɓangare, shi ne wannan dabara za ta tabbatar da ingancin muhalli, da kyautatuwar zaman rayuwar jama’a, wadda ta dace da tunanin ƙasar Sin na raya kasa, gami da babbar manufar ƙasar a fannin hulda da sauran ƙasashe, wato “amfanin kowa”.

A shekarun baya, ci gaban da ƙasar Sin ta samu a fannin kare muhalli ya burge al’ummun duniya. Muna da imanin cewar, ta hanyar haɓaka hadin gwiwar Sin da Afirka a fannin kare muhalli, za a samu damar kyautata muhallin ƙasashen Afirka, da inganta zaman rayuwar jama’ar ƙasashen.

Fassarawa: Bello Wang