Haɗin kan Afirka da Sin na tabbatar da tsaron abinci a Nahiyar Afirka

Daga BELLO WANG

A kwanakin baya an kawo ƙarshen taron ƙolin ƙungiyar AU na 35 a ƙasar Habasha, inda mahalarta taron suka sanya wa shekarar 2022 da muke ciki taken “shekarar tabbatar da samun isashen abinci masu gina jiki”, don jaddada muhimmancin tsaron abinci a nahiyar Afirka. Haƙiƙa a cikin shekarar da ta gabata, annobar COVID-19 ta haifar da mummunar illa ga tattalin arzikin ƙasashen Afirka, lamarin da ya sanya mutanen ƙasashen kimanin miliyan 30 zuwa miliyan 40 fuskantar yunwa. Wannan yanayi ya haɗa da bala’i daga indallahi, sun sa ake fuskantar ƙaruwar matsalolin rashin tsaron abinci da ta kai fiye da kashi 60%. Ganin wannan mawuyacin halin da mutanen ƙasashen Afirka ke ciki, ya sa ni, a matsayin wani Basine, fara tunanin matakan da ƙasar Sin za ta iya ɗauka, don taimaka wajen daidaita lamarin.

Sannan bayan da na yi nazarin kan wasu bayanan da aka gabatar, na gamsu da huldar ƙut-da ƙut da ake samu tsakanin ɓangarorin Afirka da Sin, ta fuskar aikin gona, inda ake ta ƙoƙarin sabunta ayyukan haɗin kai a tsakaninsu. A taron dandalin haɗin gwiwar Sin da Afirka da ya gudana a Senegal bara, ƙasar Sin ta yi alƙawarin tura ƙarin ƙwararru masu fasahohin aikin gona 500 zuwa ƙasashen Afirka, da ba da tallafin wasu ayyukan rage talauci da raya aikin gona guda 10 a nahiyar Afirka.

Don tabbatar da tsaron abinci, ya kamata a samar da ƙarin amfanin gona. A wannan ɓangare, haɗin gwiwar ɓangarorin Afirka da Sin a fannin fasahar aikin gona na taka muhimmiyar rawa. Misali a ƙasar Tanzania, farfesan jami’ar aikin gona ta ƙasar Sin, mista Li Xiaoyun, ya yi ƙoƙarin yayata wata sabuwar fasahar noman masara, wadda ta ba manoman ƙasar damar samu ƙarin masara ba tare da zuba kuɗi don sayen magani da taki ba. Kana a Sao Tome da Principe, Xu Dazhou, wani ƙwararre ɗan ƙasar Sin a fannin aikin gona, ya horar da ma’aikata masu fasahar aikin gona na ƙasar kan bambanta cututtukan da su kan kama amfanin gona, da koyar da manoma yadda ake zabar maganin kashe ƙwari mai dacewa, ta yadda aka tabbatar da ingancin amfanin gona, da samun ƙarinsu. Sa’an nan a ƙasar Mozambique, manoman wurin sun yi amfani da na’urori masu sarrafa kansu kirar kasar Sin wajen dasa iri, da fesa magani, inda aka samu damar ƙara saurin aiki, da sanya yawan hatsin da ake samu ya ninka. Waɗannan abubuwa na cikin labarun da na karanta a kwanakin nan.

Ban da samar da ƙarin amfanin gona, ya kamata a yi ƙoƙarin kyautata ayyukan noma, idan ana son tabbatar da tsaron abinci. Don cimma wannan buri, ana buƙatar sayar da amfanin gonan da wani farashi mai kyau, da samarwa manoma da ƙarin kuɗin shiga, ta yadda za su so havaka ayyukansu na samar da amfanin gona. A wannan ɓangare, ƙasar Sin ita ma na taka rawar gani, ta hanyar shigo da dimbin amfanin gona daga ƙasashen Afirka. Yanzu haka, kasar Sin ta zama ta biyu a duniya, a fannin shigo da amfanin gona daga nahiyar Afirka, inda karin kayayyaki, irinsu riɗi, da gahawa, da yaji, da lemu, na shiga cikin kasuwannin ƙasar, har ma adadin kayayyakin ya ƙaru da kashi 9.4%, a watanni 11 na farko na shekarar 2021. An ce, yadda kasar Sin ke shigowa da amfanin gonan Afirka na taimakawa nahiyar wajen daidaita illar annoba, da samun farfaɗowar tattalin arziki cikin sauri.

Sa’an nan don cimma burin tabbatar da tsaron abinci, ana buƙatar daidaita wasu matsalolin dake bayan aikin gona, misali: tashin hankali. Hukumar abinci ta duniya ta gabatar da jerin sunayen wuraren da ke fama da yunwa, ciki har da wasu ƙasashe 3 dake nahiyar Afirka, wato Nijeriya, Habasha, da Sudan ta Kudu. Dalilin da ya sa haka shi ne domin ana ta samun tashin hankali a waɗannan ƙasashen 3. Misali, a arewa maso gabashin Nijeriya, yake-yaken da ƙungiyar Boko Haram ta ƙaddamar sun sa kimanin mutane miliyan 4.4 fuskantar matsalar tamowa.

To, ta yaya za a iya daidaita wannan matsala? Za a iya ci gaba da dogaro kan haɗin gwiwar da ake yi tsakanin Afirka da Sin. Babbar manufar ƙasar Sin a fannin haɗin kai da ƙasashen Afirka kan ayyukan tsaro ita ce “Bari ƙasashen Afirka su gabatar da buƙata, da ɗauki mataki bayan da ƙasashen Afirka sun amince da haka, da baiwa ƙasashen Afirka matsayi na jagora”. Kana ƙasar tana neman daidaita matsaloli daga tushensu, inda ta mai da raya tattalin arziki cikin manyan ayyuka na tabbatar da zaman lafiya da tsaro. Aikin tsaro yana da matuƙar muhimmanci ga wata ƙasa, don haka yayin da suke kula da aikin, ƙasashen Afirka na buƙatar haɗin gwiwa da abokan hulɗa da za su iya dogaro a kansu, kana ƙasar Sin daya ce daga cikin abokan.

Abun da ya fi muhimmanci shi ne Sinawa su ma sun taba fama da yunwa. Har yanzu mamata ba ta manta da lokacin da take jin yunwa har ma ta kasa yin barci ba, a lokacin da take ƙarama. Ko da yake Sinawa sun daidaita matsalar yunwa daga tushenta, ta hanyar yin gyare-gyare da buɗe ƙofar ƙasar, da raya tattalin arizki, da fasahohin noma, gami da ƙoƙarin tabbatar da wadatar bai ɗaya ta ɗaukacin al’ummar ƙasar, amma duk da haka, mutanen Sin na ci gaba da nuna sahihanci da karamci, yayin da suke ba da taimako ga abokansu da suke fama da matsalar yunwa.