Habasha ta samu kuɗin shigar da ya kai Dala miliyan 104 daga yankunan masana’antun da Sin ta gina

Daga CRI HAUSA

Habasha ta samu kuɗin shigar da ya kai dalar Amurka miliyan 104, daga fitar da kayayyakin da aka samar a yankunan masana’antu da Sin ta gina a ƙasar.

Daraktan yaɗa labarai na yankin masana’antun na Habasha Henok Asrat, ya ce an samu kuɗin ne daga kayayyakin da aka fitar cikin watanni 6 na farkon shekarar kuɗin ƙasar da ake ciki ta 2021/2022, wadda ta fara daga ranar 8 ga watan Yuli.

Henok Asrat ya ƙara da cewa, aikin ginin yankin masana’antu na Semera dake gabashin ƙasar, da kamfanin ƙasar Sin na CCCC ke gudanarwa, ya kai kaso 97 na kammaluwa.

Ya ce Habasha na da burin ginawa da ƙaddamar da yankunan masana’antu sama da 30 a faɗin ƙasar, zuwa shekarar 2025, domin cimma burinta na zama cibiyar sarrafa kayayyaki ta zamani.

A cewarsa, gwamnatin Habasha na ba da muhimmanci ga haɗin gwiwa da kamfanonin ƙasar Sin a fannoni daban-daban.

Wannan a cewarsa, ya shafi gina yankunan masana’antu da jarin da manyan kamfanonin ƙasar Sin suka zuba a cibiyoyin masana’antu daban-daban, waɗanda aka gina galibinsu bisa mizani da kuma kuɗin daga ƙasar ta Sin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *