Roma ta fara neman sabon koci domin maye gurbin Iɓan Juric da ta ke fatan sallama idan har ya gaza yin nasara a wasa na gaba da ƙungiyar za ta kara da Torino.
Erik ten Hag ya so ɗauko tsohon ɗan wasan gaban Manchester United mai shekara 33, Danny Welbeck, daga Brighton, a lokacin da ya ke horas da United ɗin.
West Ham ta fuskanci tangarɗa a shirin ta na ɗaukar ɗan wasan gaban Atalanta mai shekara 27, Ademola Lookman, don kuwa Paris St-Germain ta yi gaba a jerin ƙungiyoyin da ke zawarcin ɗan wasan Nijeriyan.
Real Madrid za ta shiga zawarcin ɗan wasan bayan Tottenham da Sifaniya mai shekara 25, Pedro Porro, 25, idan ta kasa ɗaukar ɗan wasan bayan Ingila da Liɓerpool, Trent Alexander-Arnold.
Kungiyoyin Saudiyya na fatan ɗaukar ɗan wasan gaban Brazil da Real Madrid mai shekara 24, Vinicius Junior, inda suke fatan dambarwar kyautar 24, Ballon d’Or za ta sa ƙwallon Turai ta fita daga ran ɗan wasan.
Dan wasan gaban Jamus mai shekara 35, Thomas Muller, na sha’awar komawa taka leda a gasar Major League Soccer ta Amurka, idan ya bar Bayern Munich.
Napoli na ci gaba da tattaunawa da ɗan wasan gaban Georgia, Khɓicha Kɓaratskhelia, inda ta ke fatan ɗan wasan mai shekara 23 zai sanya hannu kan sabuwar kwangila ta yuro miliyan 84.
Ruben Amorim ya fara tattauna tsarin kwangilar sa da Manchester United kuma ba ya zaton zai yi aiki da wasu ’yan wasan ƙungiyar da suka haɗa da Antony da Casemiro da Christian Eriksen da kuma ɓictor Lindelof.
Amorim ya ce da alama zai jinkirta har sai a watan gobe kafin ya kammala komawa United, bayan an dawo daga hutun wasannin ƙasashe.
Barcelona na sha’awar ɗan wasan gefen AC Milan mai shekara 25, Rafael Leao, bayan ɗan ƙasar Portugal ɗin ya daina samun damar taka leda yadda ya saba a San Siro.
Manchester City ta ƙi amincewa da tayin da ƙungiyoyi da dama suka gabatar mata kan ɗan wasan tsakiyar ta mai shekara 18, Claudio Echeɓerri wanda ake sa ran zai koma ƙarƙarshin tawagar Pep Guardiola a 2025 daga Riɓer Plate, inda ya ke zaman aro.