A watan Junairu mai zuwa ne Real Madrid za ta yi huɓɓasar ɗauko ɗan wasan baya na Ingila, mai taka leda a Liverpool Alexander-Arnold, wanda kwantiragin sa zai ƙare a ƙarshen kakar wasa.
Sai dai Liverpool, na shirin ƙin amincewa da tayin farko kan ɗan wasan a watan Junairun.
Kungiyoyin Arsenal, Liverpool da Tottenham na son ɗan wasan tsakiya na Sweden mai taka leda a Eintracht Frankfurt Hugo Larsson mai shekara 20.
A watan Junairu ne ake sa ran Crystal Palace za tayi shirin sayen ɗan wasan tsakiya na Ingila ajin ‘yan ƙasa da shekara 18, da ke taka leda a Sunderland, Chris Rigg, mai shekara 17 kan farashin fam miliyan 20.
Everton ta nuna sha’awar ɗan wasan baya na Ghana mai taka leda a Brighton Tarik Lamptey mai shekara 24 idan kwantiraginsa ya ƙare an kuma buɗe kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa.
Al-Hilal na duba yiwuwar soke kwantiragin ɗan wasan gaba na Brazil Neymar a watan Junairu, Al-Hilal na son maye gurbin ɗan wasan mai shekara 32, da ɗan wasan gaba na Portugal Cristiano Ronaldo mai shekara 39 da yake taka leda a ƙungiyar Saudiyya.
Manchester United da Chelsea na sahun gaba na son ɗauko ɗan wasan Sweden da Sporting Viktor Gyokeres mai shekara 26, a kaka mai zuwa.
A kaka mai zuwa dai farashin Gyokeres zai kai fam miliyan 63, fiye da adadin da aka yi hasasshe na fam miliyan 20 tun da farko.
Manchester United na son ɗan wasan tsakiya na Jamus, mai taka leda a Bayern Munich Leon Goretzka, mai shekara 29.
Tottenham na sha’awar ɗan wasan tsakiyan Netherlands Tijjani Reijnders, mai shekara 26, amma ba sa tunanin za su iya cire shi daga AC Milan a watan Janairu.
Chelsea ba za ta yi tunanin sayar da ɗan wasan baya Benoit Badiashile, mai shekara 23 ba, yayin da ta ke shirin ci gaba da riƙe ɗan wasan na Faransa na dogon lokaci.
Nottingham Forest na son ɗaukar ɗan wasan Bayern Munich Mathys Tel, mai shekara 19, a matsayin aro amma ɗan wasan na Faransa na kasa da shekara 21 ba shi da shirin barin Baɓaria a wannan hunturun.
Tsohon kocin Chelsea da Everton, Frank Lampard, ya bayyana a matsayin ɗan takarar karɓar ragamar aiki daga kocin AS Roma Ivan Juric, idan har ƙungiyar ta yanke shawarar rabuwa da kocin ɗan ƙasar Croatia.
Tottenham za ta fara nazarin ƙara shekara guda kan kwantiragin ɗan wasan gaban Koriya ta Kudu Son Heung-min, mai shekara 32.
Manchester United za ta tattauna da sabon kocinta Ruben Amorim kafin yanke shawara kan kwantaragin ’yan wasan da ke daf da kammala kwantiraginsu.
Aston villa na daf da ƙulla sabuwar yarjejeniya mai tsoka da ɗan wasan gaban Ingila Morgan Rogers, mai shekara 22.