Hada-hadar kasuwar ’yan wasan ƙwallon ƙafa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ɗan wasan tsakiya na Arsenal da Norway Martin Odegaard na shirin ƙulla sabuwar yarjejeniya da ƙungiyar kasancewar kwantiraginsa na yanzu zai kare a 2025.

Kocin Bayer Leverkusen Xabi Alonso ya bayar da tabbacin ci gaba da zama a ƙungiyar ta Jamus a kaka ta gaba bayan da aka riƙa danganta tsohon ɗan wasan na Liverpool da aikin kocin Tottenham da ba kowa a yanzu.

Ɗan wasan Arsenal Albert Sambi Lokonga, mai shekara 23, zai so tafiya Burnley domin sake haɗewa da kociya Vincent Kompany, wanda ya koyar da ɗan Belgium ɗin a Anderlecht.

Ɗan wasan Ivory Coast Wilfried Zaha na tunanin ci gaba da zama a Crystal Palace, kasancewar kwantiraginsa zai ƙare a bazaran nan.

Barcelona za ta sake yunƙurin sayen ɗan wasan tsakiya na Real Sociedad da Sifaniya Martin Zubimendi, mai shekara 24, a bazaran nan bayan da rahotanni suka ce Arsenal ta ƙasa sayensa a watan Janairu da tayin fam miliyan 53.

Ɗan gaban Senegal Sadio Mane, na son ci gaba da zama a Bayern Munich duk da rikicin da suka yi da Leroy Sane a watan Afirilu.

Tsohon kocin Bayern Munich Julian Nagelsmann ne zabin farko da zai maye gurbin Graham Potter, a matsayin kocin Chelsea, in ji wakilin Bajamushen.

Kocin Liverpool Jurgen Klopp na son riƙe ɗan wasansa na tsakiya James Milner, ɗan Ingila mai shekara 37, wanda ke shirin barin ƙungiyar, domin ba shi aikin horar a ‘yan wasa.

Manchester United ta cimma matsaya da ɗan bayan Napoli Kim Min-jae na Koriya ta Kudu.

Arsenal na shirin taya Declan Rice na West Ham fam miliyan 92, kudin da Gunners ɗin ba su taɓa kashewa ba a sayen ɗan wasa a tarihi.

Bayern Munich ma na sha’awar Rice domin kocinta Thomas Tuchel na ƙoƙarin ƙarfafa tsakiyar ƙungiyar.

Haka kuma kociyan Arsenal ɗin Mikel Artetana son ɗan bayan Manchester City da Portugal Joao Cancelo, wanda yanzu yake zaman aro a Bayern Munich, amma kuma Arsenal ɗin na ganin da wuya City ta yarda ta sayar mata da shi a bazaran nan mai zuwa.

Paris St-Germain na son Manchester City ta sayar mata da Bernardo Silva, bayan da cinikin ɗan wasan na tsakiya ɗan Portugal ya ƙi kayawa a bazarar da ta wuce, ana ganin farashinsa a yanzu zai kai kusan fam miliyan 70.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *