Hada-hadar kasuwar ’yan wasan ƙwallon ƙafa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ɗan wasan gaba a Portugal Cristiano Ronaldo na son barin ƙungiyar Al Nassr ta Saudiyya, babu mamakin ya dawo Turai.

Juventus ta jadadda cewa ɗan wasanta, Dusan Vlahovic mai shekara 23 daga Serbia ba na sayarwa ba ne, ta fitar da wannan sanarwa ne ganin rububin da aka soma a kansa.

Ƙungiyar Fenerbahce ta Turkiyya na kan gaba a cinikin saye ɗan wasan Belgium da Ac Milan Divock Origi, wanda ke cika shekara guda da barinsa Liverpool.

Tottenham na duba yiwuwar tuntuɓar kocin Feyenoord, Arne Slot.

Slot na iya zama sabon kocin Tottenham idan aka daidaita da wakilansa a ranar Laraba.

Tottenham ta alƙawartawa Slot cewa za ta ba shi ƙarfin iko a yarjejeniyar.

Newcastle United za ta gudanar da taro a wannan makon domin yanke hukunci kan ‘yan wasan da za ta siyo, sai dai akwai matsalar kuɗi da ka iya shafar cinikinta da ‘yan wasan.

Manchester United na duba yiwuwar ɗauko sabbin ‘yan wasan gaba biyu – sai dai ba ta da tabbacin ko za ta iya daidaitawa da Tottenham kan ɗan wasan Ingila, Harry Kane mai shekara 29.

Ɗan wasan Ajax asalin ƙasar Ghana Mohammed Kudus, wanda ake alakantawa da Arsenal, Manchester United da Newcastle United ya yi watsi da tayin tsawaita zamansa a ƙungiyar, kuma wakilinsa na ganin a yanzu lokaci ya yi da zai sauya sheƙa.

Everton na shirin sayar da ɗan wasanta Amadou Onana kan yuro miliyan 60 domin cike givin cinikin kaka.

Jules Kounde ɗan kasar Faransa ya faɗa wa Barcelona cewa yana son tafiya, sai dai ƙungiyar ta La Liga za ta amince da hakan ne idan za a saye shi kan yuro miliyan 80.

Arsenal a shirye take ta sayar da ‘yan wasa kusan takwas a wannan kaka, yayin da take harin ‘yan wasa da dama ciki har da James Maddison na Leicester City mai shekara 26, da Declan Rice na West Ham mai shekara 24.

Ƙungiyar na kuma son ɗauko ɗan wasan Jamus Ilkay Gundogan mai shekara 32, idan bai cimma sabon kwantiragi na Manchester City ba.

Real Madrid ta sanya sunan Kyeftin ɗin Liverpool Andy Robertson mai shekara 29 a jeren ‘yan wasan da take tunanin za su iya maye gurbin Ferland Mendy mai shekara 27.

Bayern Munich ta nuna kwaɗayinta kan ɗan wasan Manchester City da ke buga gaba, Julian Alvarez, mai shekara 23.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *