Hada-hadar kasuwar ’yan wasan ƙwallon ƙafa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Everton na son ɗan wasan Faransa Moussa Dembele, mai shekara 27, da kuma mai bugawa Leicester, Jamie Vardy, mai shekara 36.

Newcastle na ci gaba da tattaunawa da Leicester kan ɗan wasanta na gefe Harvey Barnes, mai shekara 25, kan fan miliyan £30.

Ɗan wasan tsakiya a Nice da Wales Aaron Ramsey, mai shekara 32, ya samu tayi mai gwavi daga Saudiyya.

Mai buga tsakiya a Tottenham da Denmark Pierre-Emile Hojbjerg, mai shekara 27, ya kasance matashin da Atletico Madrid ta jima tana zawarci.

Chelsea a shirye take ta sayar da Trevoh Chalobah, mai shekara 24, a wannan kaka muddin ta samu tayi.

Manchester City ta yi watsi da tayin da aka gabatar mata na fan miliyan 30 kan ɗan wasanta da ke buga tsakiya James McAtee, mai shekara 20.

Bristol City ta yi watsi da tayin fan miliyan 15 daga Bournemouth kan ɗan wasanta mai shekara 19, Alex Scott.

Mai tsaron baya a Manchester United Will Fish, ɗan shekara 20, ya amince ya sake komawa Hibernian zaman aro.

Wolves a shirye ta ke ta karvi tayi kan Jonny Castro Otto, mai shekara 29, yayinda take tattaunawa kan sake dawo da ɗan wasan Jamhuriyar Ireland, Matt Doherty, mai shekara 31.

Ɗan wasan tsakiya a Chelsea da Amurka, Christian Pulisic, mai shekara 24, zai sanya riga mai lamba 11 idan ya koma AC Milan.

Liverpool a shirye take ta gabatar da tayi kan ɗan wasan Chelsea da Ingila, Levi Colwill, mai shekara 20.

Manchester United da Newcastle United da Aston Villa na zawarcin ɗan wasan gaba a Atletico Madrid da Portugal, Joao Felix, mai shekara 23.

West Ham ta soma fusata kan cinikin ɗan wasanta na tsakiya Declan Rice, mai shekara 24, da take neman fan miliyan 105, sakamakon tsaikon da ake cin karo da shi daga ɓangaren lauyoyin Arsenal da ke shirya takardun kwantiragin.

Kyeftin ɗin Liverpool, Jordan Henderson na duba yiwuwar komawa ƙungiyar da Steven Gerrard ke horar wa wato Al-Ettifaq ta Saudiyya. Har yanzu dai ba su kai ga tuntubar ɗan wasan mai shekara 33, amma dai sun nuna sha’awarsa za su saye shi.

Paris St-Germain za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta mallaki ɗan wasan Tottenham da Ingila Harry Kane, mai shekara 29, duk da dai hankalinsa ya fi karkata ga Bayern Munich.

Barcelona na son saye ɗan wasan tsakiya a Manchester City da Portugal Bernardo Silva, mai shekara 28, amma kuma suna son tuntubar ɗan wasan Tottenham da Argentina, Giovani lo Celso, mai shekara 27, koda za a samu matsala.

Nottingham Forest na farautar ɗan wasan da suka jima suna zawarci wanda ke taka leda a PSV Eindhoven asalin Ivory Coast Ibrahim Sangare, mai shekara 25.

Ɗan wasan tsakiya a Juventus da Faransa Paul Pogba, mai shekara 30, ya samu tayin fan miliyan 128 na kwantiragin shekara uku daga Saudiyya.

Mai bugawa Tottenham da England Harry Kane ya matsu kan tafiya Bayern Munich a wannan kaka, yayinda ƙungiyar ta Bundesliga ke shirin sake miƙa tayi a karo na uku kan ɗan wasan mai shekara 29.

Bournemouth ta sha gaban Tottenham da West Ham da Wolves a cinikin ɗan wasan Bristol City da Ingila mai buga tsakiya, Alex Scott, ɗan shekara 19.

Viktor Gyokeres na shirin barin Coventry zuwa Sporting Lisbon nan da ‘yan kwanaki, inda ƙungiyar ta Championship ke saran samun fan miliyan 20 da rabi kan matashin mai shekara 25 asalin Sweden.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *