Hajjin 2021: Babu kujerar Hajji da aka bai wa Nijeriya – inji NAHCON

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON) ta kore batun da aka yi ta yayatawa wai ta samu kujerun Hajji daga Gwamnatin Saudiyya na Hajjin bana.

Sanarwar da hukumar NAHCON ta fitar a Juma’ar da ta gabata wadda ta samu sa hannun shugabar sashen hulɗa da jama’a ta hukumar, Fatima Sanda, ta nuna hankalin hukumar ya kai ga wani saƙon talla da aka yi ta yaɗawa a soshiyal midiya kan cewa Nijeriya ta samu gurbin mahajjata 50,000 na Hajjin 2021/1442 AH a hukumance.

Tallar ta buƙaci maniyyata Hajji suna iya soma ajiyar wani kaso na kuɗi don sayen kujerar Hajji.

Da wannan ne hukumar ta ce tana sanar da al’umma cewa wannan batu ba gaskiya ba ne.

A cewar NAHCON, “Babu wani tsari da Saudiyya ta sanar da NAHCON game da sha’anin Hajjin bana, balle kuma ba ta gurbin kujerun Hajji.

“Duk lokacin da hakan ya faru, NAHCON ba za ta ɓata lokaci ba wajen bayyanar da komai a hukumance da kuma tsarin yadda za ta yi rabon kujerun da aka samu ga jihohi.”

Don haka, shugaban NAHCON ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga ‘yan Nijeriya da a yi hattara gudun kada a faɗa a komar ‘yan damfara.

Ya ce duk mai buƙatar ya soma biyan wani kaso na kujerar Hajjin 2021, sai a ziyarci Hukumar Walwalar Alhazai a jiha, ko kuma shafin intanet na hukuamar: https://nigeriahajjcom.gov.ng/umrah-licensed-companies/ ko kuma www.nigeriahajjcom.gov.ng domin duba jerin kamfanonin da aka amince musu yin jigilar maniyyata.

A ƙarshe, NAHCON ta jaddada cewa lallai ne jama’a su yi fatali da labarin da ba shi da tushe, sannan a saurara sai zuwa lokacin da hukumar za ta bada sanarwa a hukumance game da Hajjin bana kafin shirye-shirye sun kankama.