Hajjin 2022: Maniyyaci zai biya kuɗin kujera sama da Naira miliyan biyu da rabi

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Hukumar Jigilar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta ayyana cewar, kuɗin kujerar zuwa aikin hajji na wannan shekara ta 2022 zai haura Naira miliyan biyu da rabi, fiye da ƙarin kashi hamsin 50 cikin ɗari na Naira miliyan ɗaya da rabi da Alhaji ya biya a shekara ta 2019.

Bisa wannan sabon tsari, maniyyata waɗanda suka biya kuɗaɗen ajiya wa hukumomin Alhazai na jihohi tun shekarar 2020, a taƙaice za su biya ƙarin fiye da Naira miliyan ɗaya domin samun damar sauke farali a ƙasa mai tsarki.

Shugaban hukumar ta NAHCON, Dokta Zikirullah Hassan shine ya sanar da wannan faɗakarwa a wani zama da ya yi da sauran shugabannin hukumar, a cikin shirye-shiryen hukumar da suka jiɓanci ayyukan hajji na wannan shekara ta 2022.

Ya bayyana cewar, hasashen ƙarin ya biyo bayan la’akari da yanayin tattalin arzikin ƙasa ko ƙasashe ne, haɗi da lamura da suka jiɓanci hakan.

Dokta Hassan sai ya ce, “hasashen qarin kuɗin kujera yana hauhawa ne la’akari da cewar, a shekara ta 2019 kuɗin canji ya kasance Naira 306 ne, amma yanzu canjin ya hau zuwa Naira 410 a Dalar Amurka ɗaya.

Shugaban hukumar ta NAHCON ya ƙara da cewar, “ƙasar Saudiyya ta yi ƙari akan kuɗin haraji daga kashi biyar zuwa kashi goma sha biyar cikin ɗari. Bayani dangane da hakan shi ne sun yi ƙarin kayayyakin sauƙaƙa ayyukan hajji a Minna da Arafat.”

Zikirullah ya bayyana cewar, kowane maniyyaci za a yi masa allurar da za ta bunƙasa kariya wa jikin sa, yayin da yin gwajin PCR zai kasance wajibi.

Dangane kuwa da yadda canjin kuɗaɗe yake hauhawa yau da kullum, yayin da tuntuni wasu suka biya kuɗaɗen kujeru, lokacin da canjin kuɗaɗe yake da ɗan sauƙi, Shugaba Hassan ya bayyana cewar, za a tantance maniyyaci a bisa tsarin wanda ya fara zuwa shine akan gaba, haɗi da tsarin biya na masu adashen gata suna da kashi sittin cikin ɗari na adadin kujeru, yayin da masu biya kai tsaye za su samu kashi arba’in cikin ɗari na kujerun.

Ya ce daga cikin adadin kujeru 43,008 da ƙasar Saudiyya ta ware wa Nijeriya, kujeru 33,976 za a raba wa jihohi, yayin da masu jigilar alhazai masu zaman kan su za su samu kujeru 9,032.

Wannan majiya ta fahimci cewar, rabon kujerun yin ayyukan hajj da ƙasar Saudiyya ta rarraba wa ƙasashe na wannan shekara yayi banbaraƙwai da adadin yawan kujeru 93,000 da aka bai wa Nijeriya gabanin ɓullowar cutar shaƙewar numfashi ta Korona.

Hukumomin ƙasar Saudiyya dai sun haramta wa ƙasashen duniya gudanar da ayyukan hajji a shekarun 2020 da 2021 saboda hana yaɗuwar cutar Korona zuwa cikin ƙasar su.

Duk da galihun samun kujerun ayyukan hajj guda 95,000 da Nijeriya a baya take samu, waɗanda daga cikin wannan adadi take warewa jihohi kujeru 75,000 da kujeru 75,000 wa jiragen ‘yan kasuwa, ƙasar da ƙyar take yin amfani da ɗaukacin kujeru da aka keve mata.

Misali, a shekara ta 2019, ‘yan Nijeriya da kaɗan da suka haura adadin maniyyata 60,000 ne suka gudanar da ayyukan hajji a ƙasa mai tsarki.