Hajjin 2022: Saudiyya ta buɗe ƙofa ga maniyyata daga sassan duniya

Daga BASHIR ISAH

Bayan shekaru biyu a jere da hana ‘yan ƙetare zuwa aikin Hajji da Umarah a Saudiyya da gwamnatin ƙasar ta yi a matsayin wani mataki na yaƙi da annobar korona, yanzu dai Masarautar Saudiyya ta bada sanarwar cewa za ta buɗe ƙofofin masallatan Makka da Madina ga mahajjata daga sassan duniya don aikin Hajji da Umara na shekarar 2022.

Tun farko, Saudiyya ta sanar a ranar Asabar da ta gabata cewa ta ɗage dokar nan ta bada tazara a tsakanin juna a cikin masallacin Harami da Madina.

Cikin wani taƙaitaccen jawabi da ya gabatar, Imam Sheikh Abdullah Juhany, ya buƙaci musulman da ke Masallacin Harami da su daidaita sahunsu kafaɗa da kafaɗa yayin sallar Subuhi ta jiya Lahadi wanda hakan wata alama ce da ke nuni da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gidan Saudiyya ta ɗage dokar bada tazara a tsakanin juna.

A jiya Lahadi Ma’aikatar Hajji da Umara ta bayar da sanarwar cewa za a bar maniyyata daga sassan duniya su yi aikin Hajjin wannan shekarar ta 1443/2022, tare da cewa sharaɗi guda ɗaya tilon da za a gindaya shi ne, tilas kowane maniyyaci ya tabbatar da ya yi allurar rigakafin korona.

A cewar ma’aikatar, “Maniyyata daga sassan duniya ne za su yi aikin Hajjin bana bayan shekaru biyu (da rashin samun zarafin haka).

“Babban sharaɗin da kowane maniyyaci zai tabbatar da ya kiyaye shi ne yin rigakafin korona.”

Kazalika, an sanar cewa nan gaba Ma’aikatar Hajji da Umara za ta bayyana adadin maniyyatan da za a bai wa kowace ƙasa damar turawa Saudiyya don Hajjin bana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *