Daga BASHIR ISAH
Hukumar Aikin Hajji ta Nijeriya, NAHCON, ta buƙaci kamfanin da ya yi wa mahajjatan Afirka daga ƙasashen da ba Larabawa ba hidima yayin Hajjin bana a Saudiyya, da ya maido da kuɗaɗen da aka biya shi.
NAHCON ta buƙaci hakan daga Kamfanin Mutawifs for Pilgrims from Africa Non-Arab Countries ne saboda gazawar kamfanin wajen yi wa alhazan Nijeriya hidima yadda ya kamata a Mina yayin aikin Hajjin 2023.
Shugaban NAHCON na ƙasa, Zaikrullah Kunle Hassan, tare da wakilan hukumomin alhazai na jihohi da kamfanonin yawon buɗe ido su ne suka buƙaci hakan bayan da suka nuna rashin jin daɗinsu dangane da rashin ingancin ayyukan kamfanin musamman a kan abin da ya shafi ciyarwa da samar da tantunan zaman alhazai yayin zaman Mina.
Sun nuna buƙatar kamfanin ya maido da kuɗaɗen ne a wajen taron da suka yi a ofishin kamfanin da ke Makka a Saudiyya.