Hajjin 2024: Gwamna Bago ya ɗauke wa maniyyatan Neja nauyin Hadaya

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya ɗauke wa maniyyatan bana a jihar nauyi hadaya yayin aikin Hajjin bana.

Gwamnan ya ɗauke wa maniyyatan nauyin ne ta hanyar biya wa kowannensu Dala 200.

Amirul Hajji na jihar, Attahiru Gunna, shi ne ya bayyana haka ga manema labarai a Minna, babban birnin jihar.

Attahiru ya ce za a maida wa maniyyatan da suka riga suka miƙa kuɗin hadayar da kuɗaɗensu.

Maniyyata sama da 3000 ake sa ran a bana za su sauke farali daga jihar.

Ya ƙara da cewa, maimakon tashi ta Abuja zuwa Saudiyya kamar yadda aka saba a baya, bana ta Babban Filin Jirgin Saman da ke Minna maniyyatan za su tashi, wanda wannan shi zai zama irinsa na farko a tarihin jihar.