Hajjin 2024: NAHCON ta sanar da ƙarin kuɗin Hajji

Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON), ta sanar da yiwuwar ƙarin kuɗin kujerar Hajji a yayin Hajjin 2024 idan Allah Ya kai mu.

Hukumar ta ce Naira miliyan 4.5 shi ne mafi ƙarancin kuɗin da maniyyaci zai iya sakawa a asusun ajiya a ƙarƙashin hukumar wanda hakan ke nuni za a fuskanci ƙarin kuɗin kujerar Hajji a 2024.

NAHCON ta ce ya zuwa yanzu tana nazarin rahotannin da kwamitoci suka gabatar mata dangane da Hajjin 2023 da ya gabata.

Da yake jawabi a wajen taron manema labarai da hukumar ta shirya a Abuja, shugaban NAHCON na ƙasa, Zikrullah Kunle Hassan, ya yi ƙarin haske kan shirye-shiryen hukumar dangane da Hajjin 2024.

Hassan ya nuna farin cikinsa dangane da nasarorin da hukumar ta samu yayin Hajjin 2023, musamman kammala jigilar alhazai 95,000 zuwa da dawowa cikin lumana duk da irin ƙalubalen da aka fuskanta.

Shugaban ya ce tabbas yayin Hajjin bara an fauskanci matsalar ƙarancin abinci da masauki a Muna wanda hakan ya haifar da kafa kwamiti na musamman wajen shawo kan matsalolin.

Ya ce tuni NAHCON ta fara shirye-shiryen Hajjin baɗi domin tabbatar da komai ya tafi yadda ake buƙata.